Abun farin ciki ya samu mai sana'ar sayar da madara

Abun farin ciki ya samu mai sana'ar sayar da madara

Babu shakka akan take kowa yayi da kyau zai ga da kyau, kuma masu iya Magana sunce alkhari danko ce tana bibiyar duk mai aikata ta. Hakane ta kasance da wani bawan Allah mai sana’ar sayar da madarar yoghurt a wata unguwa dake jihar Kaduna.

Shi dai mutumin ya kasance yana sana’ar sayar da madarar yoghurt ne a wata unguwa dake jihar Kaduna. Ya dauki tsawon shekaru 30 a wannan sana’a tasa, kuma ya kasance shi mutum nai mai alkhari da kyautata wa yara kanana, har ta kai ya kan ba yaran kyautar madarar idan basu da kudi.

Ana cikin hakan ne aka wayi gari shima abun alkhairin da yake aikata wa jama’a ta dawo garesa, lokacin da wani abokin cinikinsa cikin yaran da yake rabawa madarar sa kyauta ya basa mamaki wanda bai taba zata ba, ba komai bace kyautar da ya basa illa takardar karban kudi a banki (cheque) ta naira miliyan uku (3).

KU KARANTA KUMA: Wani Alhaji yayi wa marainiya ciki a jihar Sakkwato

wanda ya masa wannan kyautar ban mamakin ba kowa bane illa daya daga cikin yaran da ya ke ba kyautar madarar sa a shekaru talatin (30) da suka wuce. wannan bawan Allah mai sana'ar yasar da madara da aka saka ma alkhairin da yayi wanda killa shi ya ma manta yayi shi yayi kukan farin ciki domin bai taba tsammanin cewa abunda ya ke aikatawa zai dawo a gareshi wata rana ba.

Ga hotuna a kasa:

Abun farin ciki ya samu mai sana'ar sayar da madara
Wani mai sana'ar sayar da madara
Abun farin ciki ya samu mai sana'ar sayar da madara
An ba mai sana'ar sayar da madara kyautan naira miliyan 3
Abun farin ciki ya samu mai sana'ar sayar da madara

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng