Yan sanda sun kama gola sakamakon an ci shi kwallaye 43
Yan sanda sun kama wani dan wasan kwallo mai suna Marko Kwiotek, dake kama gola a kasar Jamani bayan an ci shi kwallaye 43 a yayin wasa tsakanin kungiyar sa SV Vonderort da PSV Oberhausen.
Wannan ci 43 da aka yi ma Marko ya isa laifi a kasar Jamani, wanda haka ya sanya yansanda suka kama shi yayin da yazo yin atisaye a filin su bayan kwanaki biyar da faruwar lamarin.
KU KARANTA: Kungiyar Barcelona tayi sabon gola
An jiyo Marko yana fada ma abokanan wasan sa yayain da yansanda suka tasa keyarsa daga filin nasu cewa kada su damu, za’a magance wata matsala ne kawai. Amma tun daga wannan lokaci ba’a kara ganinsa ba, kuma yansanda ba suyi bayanin dalilin kama shi ba.
Gab da zuwan yan sanda domin su kama shi, an jiyo Marko yana fada ma abokansa “gaskiya ban ji dadin sakamakon wasa tsakanin mu da kungiyar Batenbrocker Ruhrpott Kicker III ba, kuma ban sa hakan ta kara maimaituwa.” Shi ko mai horar da kungiyar su Marko Yvonne Liesenfeld yace “ban san abin da yansanda ke nufi ba, da farko dai an ci shi kwallaye 43, sai kuma gashi hukuma ta kama shi.”
Sai dai mu a nan gida Najeriya, abinda da Marko yayi baa bin mamaki bane, tunda an taba samun kungiyar kwallo a Najeriya da aka ci kwallaye 79 da nema a shekarar 2013. Jaridar Goal.com ta ruwaito kungiyar Plateau United Feeders ta zarga ma Akurba FC ci 79-0, inda su kuma kungiyar Machine FC suka lallasa Babayaro FC ci 67-0 a wasu wasannin da duk wanda yaci zai haura zuwa ga gasar rukuni na uku na cin kofin firimiya na kasa. Duk da haka, dakatar da kungiyoyin kawai akayi, ba kama su ba.
Asali: Legit.ng