Wani Alhaji yayi wa marainiya ciki a jihar Sakkwato

Wani Alhaji yayi wa marainiya ciki a jihar Sakkwato

Wani dan jaridar Najeriya dake aiki tare da gidan radiyon DW na kasar Jamus, Faruk Muhammad Yabo, ya bayyana wani labara mai taba zuciya a shafin zumunta na Facebook.

Ya yada hoton wata matashiyar yarinya marainiya wacce ke dauke da cikin wata takwas (8) da wani Alhaji yayi mata a jihar Sakkwato. Karanta labarin a kasa:

Wani Alhaji yayi wa marainiya ciki a jihar Sakkwato
Marainiya Maimuna

 “Labarin wannan matashiya mai karancin shekaru, Maimuna wacce ta kasance marainiya a kauyen Birnin ruwa dake jihar Sakkwato, wani Alhaji Giwa wadda suka fito daga kauye daya ne yayi mata fyade har ciki ya shiga, daga bisani ya tafi ya barta, labarin abun tausayi ne. maimuna dake dauke da cikin wata 8 bata da kowa da zai dauki nauyin cikinta a yanayinda take ciki na karanci shekaru. Yanzu bata da madafa tunda mahaifinta ya dade da rasuwa, kuma mutumin da ake zargin yayi mata ciki ya karyata a gaban kotun shari’a na jihar Sakkwato cewa bashi yayi mata cikin ba, amma Maimuna ta dage kan cewa Alhaji Giwa ne yayi mata cikin.

KU KARANTA KUMA: Lafiya uwar jiki: Cutar daji (cancer)

 “Masu bada shaida guda biyu wadanda suka fito daga kauye daya sun rantse a gaban kotu cewa Alhaji Giwa ya fada masu cewa zai dauki Maimuna ya kaita gurin gwani a fannin zubar da ciki, domin a zubar mata da ciki, amma daga baya ya canza ra’ayin sa. Yarinya talakawa, Maimuna ta na tsananin bukatar taimako daga hukumar kare hakkin mutane saboda Alhaji mutumin da yayi mata ciki ya rigada ya dauki Lauya kan shari’ar"

Abun tausayi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng