Arewa na bukatan dalar gyada don cigaban tattalin arzikin ta?

Arewa na bukatan dalar gyada don cigaban tattalin arzikin ta?

A zamanin baya lokacin da ake amfani da shugabancin yakuna, tsakanin 1959-1966 tattalin arzikin kasar Arewa ya dogara ne kacokan da harkar noma, musamman ma irin kayyakin amfanin gona da ake fitarwa kasashen waje.

Arewa na bukatan dalar gyada don cigaban tattalin arzikin ta?
dalar gyada a Kano

Daga siyar da amfanin noman ne gwamnatin Arewa ke samun kudaden shiga da take amfani dasu wajen gudanar da aikace aikacen ta kamar su samar da hanyoyi, ruwan sha, asibitoci, makarantu har ma da bunkasa ilimi da dai sauran aikace aikacen gwamnati.

Daya daga cikin ireiren kayayyakin amfanin gonar kuwa shi ne Gyada, a wancan lokacin akwai abinda ake kira ‘Dalar gyada’, ita dai dalar gyada wani shiri ne da ake yi ma buhuhunan gyada inda za’ayi ta daura buhu daya kan daya har sai sun kai kololuwa. Asali ma a Kano ake samun dalar gyada, dalar gyada ta shahara a wancan zamani da har turawa kan zo yawon bude idanu don ganin ma idanunsu.

Tarihi ya nuna cewa Alhaji Alhassan Dantata, wato kakan Aliko Dangote, wanda ya kasance hamshakin attajiri ne a wancan lokaci, shi ya fara gina dalar gyada, a lokacin shi ne ke sayar ma kamfanin ‘Royal Niger Company’ (RNC) da gyadan da suke sarrafawa a can kasar Ingila.

Arewa na bukatan dalar gyada don cigaban tattalin arzikin ta?
Aminu Dantata yaron Alhassan Dantata tare da Aliko Dangote
Arewa na bukatan dalar gyada don cigaban tattalin arzikin ta?
Alhassan Dantata

Saboda wannan cinikayya dake tsakanin Dantata da RNC, sai ya sa ana tara mai gyadansa a tsarin dala a Kofar Nasarwa, inda wasu attajirai masu harkar gyadan suma sai su tara nasu dalar a unguwanni kamar su Birget, Kofar Mazugal, Bebeji, Malam Madori da Dawakin Kudu kusa da layin dogo domin samun saukin tafiyar da gyadan a cikin jirgin kasa, kowanne dala na dauke da akalla buhu 1500 na gyada.

KU KARANTA: Abin da yasa shinkafa tayi tsada - Minista Audu Ogbeh

Sai dai kash! Tun bayan bayyanar man fetur a tsakanin shekarun 1960s-1970s, sai akalar tattalin arzikin kasar nan ta koma kan mai, da haka ne jama’a sukayi watsi da noma, sanadiyyar haka sai ya zamana babu sauran dalar gyada a ko ina. Duk da irin kokarin da gwamnatoci sukayi na ganin sun dawo da dalar gyada amma hakan ya ci tura.

Sai dai, masana sun nuna cewa yankin Arewa bata bukatar dawowar dalar gyada kafin tattalin arzikin ta ya bunkasa. Dalili kuwa shi ne, misali ka duba farashin gwangwanin gyada, da farashin gwangwanin man-gyada, na tabbata bambamcin farashin ba kadan bane, saboda tabbas farashin gwangwanin man gyada ya dara na gwangwanin gyada. Tambayar anan shi ne mai zai sa wani can ya fi samun ribar amfanin noma fiye da manomin kan shi?

Arewa na bukatan dalar gyada don cigaban tattalin arzikin ta?

Ba kasar da zata taba samun cigaba idan abin data kware shi ne ta siyar da kayayyakin amfanin nomanta, bincike ya nuna, kasa na samun cigaba ne ta fannin tattalin arziki idan tana sarrafa amfanin nomanta da kanta, sa’annan ta fitar dasu, idan akayi haka an samu isashshen amfanin wannan kayan noma, sa’annan hakan zai samar da ayyukan yi, daga karshe kuma a samu kudaden shiga masu dimbin yawa ta hanyar siyar ma kasashen waje.

Don haka, abin da Arewa take bukata shi ne yawan masana’antun sarrafa amfanin gona, wadannan masana’antun sune zasu siya amfanin gonar daga hannun manoma a kudi ma kyau, sa’nnan su sarrafa su a kamfanunuwarsu, kaga sun samar ma mutane ayyukanyi, sai su cire dukkanin kayan amfani daga jikin wadannan amfanin gona, kaga anan an karu da amfani da dama, daga nan kuma sai su fitar da shi kasuwa, da kasashen waje domin siyarwa, kaga gwamnati zata karu dasu ta hanyar biyan haraji.

Misali, idan manomi ya siyar ma kamfani gyadarsa, sai kamfanin nan ta debi ma’aikatan da zasu sarrafa mata gyadar tana biyansu albashi, da aka sarrafa gyadar, sai aka ware man-gyada, tunkuza, da bawon gyada, daga bisani sai aka siyar da man gyadan a kasuwannin mu da na kasashen waje, ta yada ba sai mun jira an shigo mana da man gyada ba daga kasashen waje, kaga an samu riba limkin ba limkin!

Toh haka ya kamata ayi ma dukkanin amfanin gonakin mu, musamman gyada, auduga, kwakwa da kwakwan manja, shinkafa, masara, waken suya, tumatir, madara, har ma da fatan dabbobi, da sauran kayayyakin masarufin da ake shigo mana dasu daga kasahen waje alhali muna dasu anan gida.

Daga karshe ina baiwa gwamnatocin jihohin Arewa shawara dasu inganta noma, ta hanyar samar da kayayyakin noma na zamani ga manoma, tare da gayyato masu zuba jari, samar da kwararru da zsu koya ma manoman sabbin hanyoyin noma na zamani, samar da iri masu inganci, da kuma samar da tsaro a gonakin mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng