An kama wani tsohon mutum yana kokarin bata wata yarinya
An kama wani tsohon mutum yana kokarin bata 'yar karamar yarinya a Abuja a kwanakin baya.
Acewar wani mai amfani da Facebook mai suna Osquare D. Okpanachi, al'amarin dai ya sanya mutanen garin Abujan jin matukar mamaki a kwanakin baya.
Tsohon mutumin wanda ake tunanin yana da shekaru 50 zuwa 60 da haihuwa a duniya, aka kamashi da wata 'yar karamar yarinya mai kimanin shekaru 4 da haihuwa yana kokarin bata ta. Ga dai abinda Okpanachi ya rubuta a shafinsa na Facebook.
"Nasan akwai shedanu a wannan garin, amman banyi tsammanin lalacewar takai haka ba, inda wani tsoho wanda yakai munzalin zama kaka yake kokarin bata karamar yarinya 'yar shekara 4 saboda talauci" .
Wannan abun ya farune a Kwali, a garin Abuja. " zuciyata tayi zafi kwarai da gaske dangane da wannan abun dana gani".
Allah ya kyauta.
Asali: Legit.ng