Shugaban Jami'a ya ziyarci Asase

Shugaban Jami'a ya ziyarci Asase

Mahaifin Tijjani Asase ya rasu, inda shugaban jami’ar NOUN ya yiwa Tijjani ta’aziya, da kuma Asase shi ne Goje a dadin kowa.

Shugaban Jami'a ya ziyarci Asase

Farfesa Abdallah Uba Adamu shugaban Jami’ar karatu daga nesa ta kasa NOUN, ya kai wa Tijjani Asase ziyayar ta'aziyya.

KU KARANTA KUMA: Sadiya Gyale ta yi bikin cika Shekara

Rahotanni na cewa, Farfesan ya kai ziyarar ce a lokacin da ake hutun bukukuwan Sallar Layya da aka yi a makon da ya wuce.

A hirarsa da Legit.ng Asase ya ce, ya ji dadin zuwan Farfesa Abdallah wanda ya je ta’aziyyar da wasu ‘yan rakiyarsa, ya kuma ce, hakika Farfesan ya karrama shi da wannan ziyarar ta’aziyya, sannan ya kuma ce, manyan mutane da yawa sun kawo mi shi irin wannan ziyarar ta’aziyyar mahifinsa, wadanda zuwansu ya ba shi mamaki matuka.

KU KARANTA KUMA: Hadiza Gabon da Adam Zango sun zama jakadu

Mahaifin jarumin wanda aka fi sani da suna Alhaji Abdu Dankura, ya rasu ne a daren 10 ga watan Satumba, wanda yayi dai-dai da ranar Arfa, an kuma yi jana’izarsa ne a ranar Sallah bayan an sauko daga Idi, a gidansa da ke unguwar Mandawari Sabon titi a cikin birnin Kano.

Tijjani Asase ya yi fice a fina-finan Hausa, a inda yawanci ya ke fitowa a matsayin mai karfi-jari, musamman a shirin wasan kwaikwayo na Dadin kowa a tashar Arewa 24, inda ya ke fitowa a matsayin Goje.

Daya daga cikin abin da ke burge mutane da mu’amalar Asase ta waje, ita ce da girmama na gaba da shi, wacce ake ganin ita ce ta sa ya yi farin jini a tsakanin manyan mutane a ciki da kuma wajen Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng