Naira ta kara daraja akan dalar Amurka

Naira ta kara daraja akan dalar Amurka

A jiya, 19 ga watan Satumba, kudin Najeriya Naira ta kara daraja akan dalar Amurka a kasuwan bankuna.

NAN ta bada rahoton cewa nairan da aka sayar a N307.25 sabanin N308.69 da aka sayar a makon da ya gabata. Amma, darajan tayi zaman dutse a kasuwan bayan fage, har yanzu dai tana N425 zuwa dala 1 kwanaki 3 kenan.

Naira ta kara daraja akan dalar Amurka

Kasuwancin nairan kuma a kasuwan canji sun nuna cewa naira bata canza ba, an kulle kasuwan ne kudi N422 akan dala,N549 akan Fam da kuma N470 akan Yuro.

Masu kasuwancin naira sun jingina canjin kudin ga wata ganawar MPC da za’a yi da bankin CBN. Suna sa ran cewa banki zata duba ka’idar canji wanda zai kawo karshen rage darajar kudin najeriyan.

KU KARANTA:Satar fasahar rubutu: Karanta abinda mai ma Buhari rubutu ke samu

A bangare guda, ministan Kudi, Kemi Adeosun tace bankuna su rage kudin ruwa saboda gwamnatin tarayya ta ari kudi a hannunsu domin bunkasa tattalin arzikin kasa, wacce take cikin tabarbarewan tattalin arziki.

Najeriya ta shiga cikin wata halin tabarbarewan tattalin arzkine a wata agusta sanadiyar ayyukan yan bindigan Neja Delta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng