Sadiya Gyale ta yi bikin cika Shekara
Jaruma Sadiya Gyale ta yi bikin cika shekara, kuma ‘yan uwa da abokan arziki nata taya ta murna, da kuma Sadiya Gyale ta canza kamanni.
A ranar Litinin 19 ga watan Satumba ne, fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Sadiya Mohammed wacce aka fi sani da Sadiya Gyale ta yi bikin cika shekara.
KU KARANTA KUMA: Arewa na bukatan dalar gyada don cigaban tattalin arzikin ta?
Hakan ya fito fili ne a shafinta na sada zumunta na Instagram, a inda jarumar ta sa wasu sabbin hotunanta, kuma ‘yan uwa da abokan arziki musamman abokan aiki a shirya fina-finai, suka rika taya ta murnar zagayowar ranar, sai dai ba ta cewa ko za ta yi walima ba ko a'a.
KU KARANTA KUMA: Hadiza Gabon da Adam Zango sun zama jakadu
A ‘yan watannin baya ne aka yi shagalin bikin auren Sadiya, bayan da ake ta rade-radin soyayyarsu da Baballe Hayatu wanda kuma ya karyata a wata hira da ya yi da BBC da cewa shi yayanta ne.
Wani abin ban sha’awa daga hotunan da Sadiya Gyale da ta sa a shafin nata shi ne, yadda jarumar ta yi kiba, ba kamar yadda aka san ta ba a fina-finanta na baya, shin ko cikar daki ne?
Asali: Legit.ng