Malamin makarantar sakandire ya lalata dalibarsa
Wani mai amfani da shafin zumunta na Facebook ya bada labarin yadda wani malamin Lissafi ya ci zarafin wata dalibarsa matashiya.
Karanta yadda ya bada labarin a kasa:
“Bai kasance sabon abu ba garemu yadda ake cin zarafin yara mata tare da bata masu dukkan rayuwar su. Yawancin yara mata sukan fara fuskantar wadannan abubuwan ne tun daga makarantar sakandire a hannun malamansu da yan bautar kasa ( wannan na daya daga cikin dalilan da ya sa ban goyi bayan tura matashi da baida da’a makarantu domin koyarwa da kuma cin zarafin yara mata a makarantun sakandiri da sunan bautar kasa ba).
“Abunda muke da shi a nan al’amari ne da ke nuna yadda muka bunkasa. Wani matashin malami, mai suna Ndubuisi Vincent, wanda ke koyar da darasin Lissafi a makarantar Nuco Comprehensive secondary school, Uyo. Ya dade yana damun daliba mai suna Idara Okon kan tayi masa alfarma ya yi lalata da ita na tsawon lokaci. Yayi amfani da shafin zumunta na Facebook gurin aika mata da sakonnin da basu dace ba. Yarinyar da taga bazata iya ci gaba da jure abunda yake mat aba tayi yanke shawarar fallasa shi ta hanyar yada hirar da sukeyi a yanar gizo don ta tura wa mutane su gani. Sai ta yada shi tare da sanya wasu malamai da dalibai da hukumomin makarantar a shafin.
KU KARANTA KUMA: Abubuwan da Kungiyar Boko Haram suka ce a sabon bidiyo
“Ina nuna kulawata ga yan Najeriya domin yaki kan cin zarafin yara kanana da kuma yara mata. Yara mata suna fuskantar kalubale da dama a kasar Najeriya. A shekara 17, ya kamata a ce ya mace ta mayar da hankalinta kan karatunta da kuma cin jarabawar WAEC, NECO, JAMB, da duk wani jarabawa da kasar Najeriya ta bata daman yi, ba wai ta dunga kwana da malamai maza wanda basu da abunda zasu bata. Wadanda suke aikata hakan sun manta dokar karma. Zasu samu yaya mata na kansu nan bada jimawa ba. Bayan haka, sun manta cewa duniyar na samun wayewar kai da ci gaba.
“Ya kamata a hukunta wannan malami akuma yanke mai hukuncin cin zarafin yarinya, cin amana da kuma duk wani laifi da ya aikata. A bari wannan ya zama darasi ga masu yin aiki irin nasa. Wadanda za’a hukunta a nan gaba sune yan bautar kasa maza wadda suke cin zarafin martabar yara da sunan bautar kasa. Ga yan bautar kasa, ina fada maku “babban yaya na lura daku.”
Asali: Legit.ng