Za a maido kudin satar Abacha Najeriya
– Kasar Amurka tayi watsi da rokon da Lauya Godwin Nanaka yake yi na a ba shi Dala miliyan $320 daga cikin kudin da Abacha ya sata
– Lauyan Kasar da ke Amurka yace hakkin sa ne a ba shi wannan kaso domin kokarin aikin da yayi wa Gwamnati
– Kotu tace sam ba zai ci wannan kudin ba
Amurka ta shirya maidowa Najeriya makudan kudin da Marigayi Janar Sani Abacha ya sata, ya kai Kasar. Labari dai sun nuna cewa, Amurka za ta maidowa Najeriya dala miliyan $550 da Tsohon Shugaban Kasa Janar Sani Abacha ya sata. Kotu ta kuma yi watsi da karar wani Lauyan Najeriya. Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Lauyan Najeriyan nan da ke Amurka, Godson Nnaka, na neman har Dala miliyan $320 daga cikin kudin Najeriyan.
Alkali John D. Bates na Kotun Amurka yayi watsi da karar Lauya Nnaka, yace ba shi da wani kaso cikin kudin. Babban Lauyan Gwamnati ya rubuta takarda ga Amurkar, inda yake neman a dakatar da Lauya Godson Nnaka daga karbar wadannan kudi. Alkali Justice Bates yace bai cancanta ya karbi wannan kudi ba, don asali ma, bai cancanta ya wakilci Najeriya ba a shari’ar. Lauya Nnaka dai bai ciwowa Najeriya shari’ar a ba a Kotu.
KU KARANTA: Shugaba Buhari na neman a ceci Kananan hukumomi
Ko kadan dai bai dace Nnaka ya wakilci Najeriya ba a wannan shari’ar, kuma maganar karbar miliyan $320 ba ta taso ba. Dole sai dai Nnaka ya kara shigar da wata karar. Yanzu dai haka, dole ma ya tattara ya bar shari’ar inji Alkalin. Wannan kuwa zai sa Najeriya ta karbe kudin ta hankali kwance.
Ministan Shari’a na Najeriya Abubakar Malami yace kawai Nnaka na kokarin bata lokaci ne wajen maido kudin Najeriya da sunan zai karbi kashi 40% na kudin. Ministan yace tun a shekarar 2004 aka dauki hayar su Nnaka sai dai ko kobo bai samu karbowa ba.
Asali: Legit.ng