Wata budurwa ta zama shugaban karamar hukuma (Hoto)

Wata budurwa ta zama shugaban karamar hukuma (Hoto)

- A kusan karon farko a Tarihi wata Budurwa ta zama shugabar karamar hukuma a Najeriya

- An nada Yarinya mai shekaru 25 a matsayin shugaban wata karamar hukuma a jihar Kebbi

- Mutanen Arugungun fa sun ce ba a taba yin haka ba, kuma ba za ayi ba

Wata budurwa ta zama shugaban karamar hukuma (Hoto)
Hindatu Umar

Jaridar Rariya ta rahoto cewa an nada wata Budurwa a matsayin Shugabar Karamar Hukumar Arugungun a Jihar Kebbi. An nada wannan budurwa ne bayan wa’adin kwamitin rikon kwaryar da aka nada ya kare. Hakan ta sa aka nada wannan budurwa mai suna Hindatu Umar mai shekaru 25 a duniya a matsayin sabuwar Shugabar Karamar Hukumar.

KU KARANTA: Uwargidar Shugaba Jonathan tayi magana

Mutanen Arugungun kuwa dai sun ce hakan ba za ta sabu ba, domin kuwa ba a taba samun haka ba a Tarihi. Sun koka da cewa ban da cewa mace ce, tana da karancin shekaru, sannan kuma ba ta san harkar Shugabancin Karamar hukuma ba ko kadan.

Ita dai wannan budurwa, Hindatu Umar ta kammala iya karatun Sakandare ne kurum. Ta yi wata makaranta da ake kira Comprehensive Secondary School. Hakan dai ya sa samarin Garin suka ce fa sam irin wannan ba za ta mulke su ba.

Mutanen Garin Arugungun dai sun ki yi wa Hindatu mubayi’a, suka ce ba a taba haka ba, asali ma kuma ma dai, ba ta cancanta ba. Ganin cewa ba ta da wani ilmin na a zo-a gani da za ta jagoranci al’umma da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng