Barin wuta tsakanin sojoji da yan bindiga

Barin wuta tsakanin sojoji da yan bindiga

-Dakarun sojojin Najeriya sun ci karfin yan bindiga a yankin Niger Delta

-Sabon aikin horo na murmushin kada da sukayi a yankin, ya yi sanadiyar mutuwar sojoji hudu

-Bangaren GOC 82, Enugu sun ce dakarun sun gudanar da ayyukan agaji a yankin

Barin wuta tsakanin sojoji da yan bindiga
Wasu daga cikin yan bindigan Niger Delta

Sojojin Najeriya sun tabbatar da mutuwan kimanin yan bindiga da masu laifi a lokacin horon da sukayi na murmushin kada a kwanan nan a yankin Niger Delta.

A rahotannin da aka ba hukumar News Agency of Nigeria (NAN) ya nuna cewa an kwato makamai iri-iri daga wadanda ake zargin yan ta’adda ne a lokacin aikin da dakarun sojoji sukayi domin dawo da zaman lafiya a yankin.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya tafi kasar Amurka

Da yake Magana kan ci gaban kwanakin nan, babban Janar Ibrahim Attahiru, kwamandan jami’ai gaba daya (GOG), na yankin 82, jihar Enugu, ya kara da cewa yan ta’adda da dama sun samu raunuka a lokacin harin, ya kara da cewa an hallaka sansani 38 wanda yake mallakin yan bindigan da matatu 91 da suke ba bisa doka ba a cikin kwanaki goma.

A lokacin da yake jimamin mutuwar sojoji hudu a lokacin aikin, GOc sin ya bayyana cewa sun yi amfani da damar sun gina alaka tare da yan farar hula ta hanyar ayyukan agaji a kauyukan dake makotakar yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng