SERAP ta bukaci a gaggauta gurfanar da Patience kotu

SERAP ta bukaci a gaggauta gurfanar da Patience kotu

Biyo bayan karar da Patience Jonathan ta shigar a kotu tana neman a sake mata wasu miliyoyin dalar Amurka da aka gano a bankin Sky, ya sa jama'a na kara kiran a gudanar da bincike a kanta.

Tun can farko hukumar EFCC ta rike wasu kamfanonin Patience Jonathan hudu da su ma tana neman a sake mata.

Da ma can ita EFCC din na binciken wani hadimin cikin gidan tsohon shugaban wato Mista Dudafa da badakar miliyoyin dalar Amurka da ya kai ga rufe ma'adanin bankin. Hakan ya sanya Patience Jonathan fitowa fili ta nuna cewa wadannan kudaden nata ne.

Bugu da kari Patience ta ma kai bankin Sky kara domin neman bin kadin kudin.

Kungiyar tabbatar da adalci ga lamuran zamantakewa da tattalin arziki, SERAP, a takaice, ta bada wa'adin kwana bakwai ga ministan shari'a Abubakar Malami ya gurfanar da Patience Jonathan gaban kotu ko kuma kungiyar da dauki matakin shari'a da zai nemi tilasta binciken Patience.

Wani rahoton bayan fage na nuna neman tunkarar gwamnatin Buhari da batu sako kudin na Patience amma wasu jami'an gwamnati suka nuna cewa batun na EFCC ne kuma gwamnatin Buhari bata sa baki a harkokin hukumar.

Kwamred Abubakar Abdulsalam, shugaban wata kungiya dake yaki da cin hanci da rashawa dake mara baya ga matsayin na SERAP tace an dade ana ganin kamar matar shugaban kasa ko gwamna na cikin tsarin mulkin Najeriya amma kuma babu wannan a tsarin mulkin kasar. Duk da haka duk wani tsarin mulkin kasar sai ka ga matan suna da ruwa da tsaki ciki, suna harka da dukiyar jama'a da aiwatar da mulki kamar dokar kasa ce ta basu.

Yace daidai ne wa'adin kwana bakawai da aka ba ministan shari'a idan kuma bai yi haka ba ya nuna ba dagaske suke ba akan yaki da cin hanci da rashawa. Idan da gaske ne ba za'a kama wannan a bar wancan ba. Kowa aka samu da laifi a taboshi.

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags:
Online view pixel