Hukumar EFCC na tuhamar Patience Jonathan
Sakamakon yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari keyi, matar Tsohon shugaban kasa, Patience Jonathan na fuskantar tuhuma cikin wani bincike da akayi na dala miliyan 31.4 wanda ake zargin na cin hanci da rashawa ne.
A cikin abun da za’a iya dauka a matsayin sabon yunkuri, hukumar yaki da hana cin hanci da rashawa (EFCC) su bibiya matar tsohon shugaban kasa sun kuma daskarar da wani asusu dake da nasaba da ita , wanda zai hana ta samun damar daukar kudi daga cikin dala miliyan 31.4 dake cikin asusun a yayinda suke gudanar da bincike a kai.
A lokacin da wasu yan Najeriyar ke yaba ma hukumar ta yaki da hana almindahanan, kan yunkurin da sukayi cikin rashin tsoro wanda zai taimaka sosai gurin shafe cin hanci da rashawa da ke addabar kasar Najeriya, wasu sun bayyana wannan yunkuri a matsayin farauta kamar yadda matar tsohon shugaban keda iko a kan kudinta tunda ba wai an rigada an kama ta da aikata wani laifi bane.
KU KARANTA KUMA: An hukunta dan Najeriya da aka kama da hodar iblis
Hukumar hana cin hanci da almindana sun bayyana cewa an nuna asusun a matsayin daya daga cikin wadanda ake zargi da aikata zamba a gaban babban kotun tarayya dake jihar Lagas amma mai ba matar Jonathan shawara, Gboyega Oduwole ta mika wani shari’a a gaban kotun, cewa wacce take karewa bata ji dadin abunda hukumar ta EFCC tayi mata ba na yunkurin daskarar da asusunta.
A bangaren Patience Jonathan
Bayan hukuncin da aka yanke a kan asusunta, Patience ta nemi kotu da hukumar EFCC sun sanya mata Katanga da hakkinta a matsayinta na yar jumhuriyyar Najeriya ta hanayar ‘bada umarnin daskarar da asusunta’ ba tare da wani umarni daga kotu ko kuma an sanar da ita ba.
KU KARANTA KUMA: Yan kauye sunyi watsi da wata mata mai ciwon kafa
Yan kwanaki kadan da yin haka, matar tsohon shugaban kasar ta rubuta wasika ga Ibrahim Magu, Shugaban hukumar EFCC tana bayyana masa cewa dala biliyan 31.4 da aka gani a asusunta na kiwon lafiyarta ne.
Asali: Legit.ng