Uwargidar Jonathan ta yi kaca-kaca da Hukumar EFCC
Uwargidar Jonathan ta yi kaca-kaca da Hukumar EFCC
Matar tsohon Shugaban Kasa Jonathan Goodluck tace Hukumar EFCC ta Kasar mai yaki da cin hanci da rashawa na nema su bata mata suna. Wani Yemi Akinbode, mai aiki tare da Matar tsohon Shugaban Kasar yace an matsa ma Madam Pateince Jonathan din da tayi bayanin inda ta samu wannan uban kudi. Ana dai tuhumar Patience Jonathan da mallakan makudan kudi har sama da dala miliyan $30. Tuni dai a baya aka rahoto cewa Patience Jonathan ta amsawa EFCC cewa itace ta mallaki wannan kudi ba wani ba. Sai dai yanzu kuma Matar Tsohon Shugaban Kasa tace karya ce ake yi mata don a bata mata suna.
Matar Tsohon Shugaban Kasa watau Patience Jonathan tace ba ta taba cewa kudin da Hukumar EFCC ta kama na ta bane, sannan kuma ba ta da irin wannan uban kudi a duniya. Patience Jonathan ta ce Hukumar EFCC ce kawai ta kirkiri wannan lamari domin ta ci mata zarafi. Hukumar EFCC ta Kasar ta bayyana cewa ta kara samun wsu kudin har dala miliyan $20 da kuma wani dala Miliyan $5 a akaun din na Patience Jonathan, sai dai Matar Tsohon Shugaban Kasar ta ce duk sharri ne kurum ake yi mata.
KU KARANTA: An yi kaca-kaca da Shugaba Buhari
Matar Tsohon Shugaban Kasa Patience Jonathan tayi tir da maganar cewar ta bude akaun a banki da sunan direbobi da masu dafa abincin ta a wancan lokaci. Patience Jonathan tace wannan karyar kare dang ice ta EFCC. Kuma har wa yau Madam Patience Jonathan tace ba ta yarda da kamfunan da su ka bada shaida a kotu ba. A jiya dai wasu kamfunan da ake zargi sun tabbatar da cewa hakika sun aikata laifin da ake zargin su da shi. Lauyan Matar Tsohon Shugaban Kasan yace za su binciki kamfanin.
Matar Tsohon Shugaban Kasa Patience Jonathan tace ba ta aikata lafin komai ba, kawai wani dalili ne ya sa ake so a ci mata mutunci.
Asali: Legit.ng