Mambobin APC, UPP sun sauya sheka zuwa PDP

Mambobin APC, UPP sun sauya sheka zuwa PDP

- Daruruwan mambobin jam’iyyar APC da UPP sun sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP a jihar Edo

- Komawar tasu ya zo ne a cikin kasa da makonni biyu ga zaben gwamna wanda aka daga zuwa ranar 28 ga watan Satumba

- Sun samu tarba daga mataimakin Shugaban jam’iyyar PDP, Emma Ogbomo

Daruruwan mambobin APC da na jam’iyyar  United Progressives Party (UPP), a jihar Edo sun sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Wannan ya faru ne cikin kasa a makonni biyu ga zaben kujerar gwamna a jihar Edo wanda ake shirin yi a ranar 28 ga watan Satumba.

KU KARANTA KUMA: An hukunta dan Najeriya da aka kama da hodar iblis

Jaridar Daily Post sun ruwaito cewa Sunny Omokaro, wani tsohon ciyaman na kungiyar mahauta Najeriya wato Butchers Association of Nigeria (BAN), ne ya jagoranci masu sauya shekar.

Omokaro yayi alkawarin kawo mahauta a jihar domin su goyi bayan jam’iyyar PDP da dan takaranta.

A cewar sa, ya koma jam’iyyar PDP ne saboda shirin da Ize-Iyamu keyi ma jihar a aikace yake kuma zai taimaka wa jihar.

KU KARANTA KUMA: Tsohuwar da ta ta kula da nakassashen danta

Patience Ehigiator, wata tsohuwar shugabar mata na jam’iyyar a jihar ce ta jagoranci mambobin UPP.

Masu sauya shekar sun samu tarba daga Emma Ogbomo, mataimakin ciyaman na jam’iyyar PDP a jihar.

Yayi kira ga sabbabin mambobi sa suyi aiki da himma domin ganin dan takarar gwamnan PDP, Pasto Osagie Ize-Iyamu ya lashe zaben.

Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta sa ranar yin zaben a matsayin 10 ga watan Satumba, amma cikin kasa da sa’oi 48 aka daga zaben. Kwamishina ya bayyana tsaro a matsayin dalilin da ya sa aka daga zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel