Yan kauye sunyi watsi da wata mata mai ciwon kafa

Yan kauye sunyi watsi da wata mata mai ciwon kafa

- Kari ya fito ma Eunice Anyango bayan ta tade a kan wani itace shekaru 24 da suka wuce

- Ba ta je asibiti ba kuma Karin ya girmama sosai

- Yan kauye sun yi watsi da ahlin ta kamar yadda suka amince da cewan an sihirceta ne

Yan kauye sunyi watsi da wata mata mai ciwon kafa
Eunice Anyango, daga Eshirumbwe dake kasar Kenya ta samu kari a kafa tun shekara ta 1992

Eunice Anyango, wacce ta fito daga kauyen Eshirumbwe dake kasar Kenya, ta na kuka neman taimako tunda al’umman garinta sun juya mata baya bayan wani babban kari ya fito mata a kafar ta.

KU KARANTA KUMA: An daga shari’ar Sambo Dasuki zuwa watan Oktoba

Matar mai shekaru 35 ta tade a kan wani itace bisa tsautsayi har ya ji mata ciwo a kashinta a shekara ta 1992. Eunice bata dauki abun da muhimmanci ba ta kuma ki zuwa asibiti, tun lokacin Karin ya fara girma a hankali har wata rana ya kai girman da hankali baya tunani.

Makwabtan ta da shugabar kauyen su masu camfe camfe sun yi watsi da Anyango, makauniyar uwarta da kuma dan ta mai shekaru 16 yayinda suka ce an sihirce ahlin gidansu.

Mabel Akiso, daya daga cikin yan kauye, ta fada ma jaridar Kenyan: “Shugabar kauyen da mataimakiyarta suna da masaniyar halin da wannan ahlin gidan suke ciki, amma basu taba yi wani abu game da hakan ba. Yawancin mutane a kauyen sun yarda cewan an sihirce ahlin gidan.”

Yan kauye sunyi watsi da wata mata mai ciwon kafa

Dan Eunice ya bar makaranta domin ya kula da mahaifiyar sa da kakarsam wani lokacin yan cocin kauyen masu tausayi sukan ziyarce su.

Eunice ta karbi allurer rigakafi domin ta magance Karin zuwa wani mataki amma abun baiyi ba, yanzu matar na bukatan taimako da burin hada wasu kudade domin a cire mata Karin dake kafarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng