Rundunar soji sun kashe masu garkuwa

Rundunar soji sun kashe masu garkuwa

Rundunar sojin Najeriya ta kashe masu garkuwa da mutane guda 7 kamar yadda ta sanar da kaca kaca da matatun man sata a jihohi daban daban a yankin Neja Delta.

Rundunar soji na 33 brigade sun kashe masu garkuwa da mutanen ne yayinda suka kai wata hari wasu kauyuka a jihar a ranan juma'a, 9 ga watan satumba.

Rundunar soji sun kashe masu garkuwa

Jaridar vanguard ta kalato daga cikin jawabin da kakakin rundunar sojin najeriya, kanal Sani Usman Kukasheka yayi, yace an sanar da rundunar sojin cewa masu Garkuwa da mutanen na dajin Lame Burra kusa da Dutsen Ganye, Gunduru da kati layin a jihar bauchi.

Jawabin tace : “A yayin wata mumunan musayar wuta , rundunar sojin ta kashe 7 daga cikin masu garkuwa da mutanen kuma ta ruguza gidansu. An kuma kwato bindigan Ak47 guda 2 da bindiga 4. Har ila yau rundunar na binciken wurin saboda cimma Wadanda suka arce.

KU KARANTA :Yaro na,da shanaye 100 sun bace – Fulani Makiyayi

Kana rundunar sojin najeriya sun kama dan boko haram

“Yanada muhimmanci ku sani cewa bayan nasarorin da aka samu a Operation FOREST KUNAMA,wanda akayi da manufar kawar da masu satan shanaye da yan daba a jihar bauchi da gombe, shugaban rundunar sojin najeriya ya umurce su da cigaba da zama a Lame- Burra.anyi wannan saboda hana Wadanda suka arce dawowa wurin.

“Hakazalika an kafa daban soji 2 a Lame da Jimi domin tabbatar da tsare dajin. Sojin na zagaye wurin lokaci bayan lokaci daga daban.

“A wata labari mai kama da haka, rundunar sojin Operation LAFIYA DOLE  tare da hadin guiwan yan banga sun kama wani dan kungiyan boko haram mai suna Adamu Damuna. Ana gudanar da bincike akansa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel