Kamfanin Wuta na bin Gwamnati bashin Naira Biliyan 86
– Shugaban Kamfanin wuta na ‘Egbin Power Plc’ Dallas Peavey, yace suna bin Gwamnatin Tarayya bashin kudi sama da Naira Biliyan 86
– Mista Peavey yace bai san yadda abin zai kasance ba nan gaba
Shugaban Kamfanin Egbin na wutan Najeriya, Dallas Peavey yace Kamfanin wutan na bin Gwamnati bashin tarin makudan kudi har sama da Naira Naira Biliyan 86, Hukumar dillancin labaran Kasar watau NAN ta rahoto wannan labari.
Peavey ya bayyana hakan ne ga manema labarai a jiya Asabar 10 ga wannan wata, a Yankin Ijebu na Garin Legas. Shugaban Kamfanin yayi wannan magana ne lokacin da Kamfanin ke gabatar da wasu kyaututtuka ga wasu ‘Yan makaranta a Jihar ta Legas. Mista Peavey yayi amfani da wannan dama ya roki Gwamnati da ta taimaka ta biya ta kudin ta domin cigaba da ayyukan da suka dace. Mista Peavey ya bayyana yadda lamarin ‘gas’ ya zama ciwon kai a harkar samar da wuta a Kasar. Peavey yace kudin da suke bin Gwamnati ya haura 86b.
KU KARANTA: TOFA!!! EFCC Ta kama Ibrahim Babangida
Shugaban Kamfanin ya bayyana cewa ya kamata ace suna bada wuta akalla na karfin megawatt 1,320 sai dai yanzu abin da ake samu bai wuce Megawatt 425 kacal ba, wanda kuwa ko rabin abin ya dace bai kai ba. Mista Peavay ya bayyana cewa tun watanni shida da suka wuce suke bin Gwamnati kudi. A cewar sa Gwamnati ba ta biya su kudin wutan da suka bada ba. Peavey yace kashi 16% na cikin abin da ya kamata a biya su ne kadai aka ba su.
Kamfanin dai na duba yiwuwar samar da wutan ta wasu hanyoyin dabam da gas domin rage matsalar da ake fama da ita. Shugaban Kamfanin yace bai san yada abubuwan za su kasance ba a nan gaba, domin akwai bashin makudan kudi.
Asali: Legit.ng