Hukumar EFCC ta kama wani Ibrahim Babangida

Hukumar EFCC ta kama wani Ibrahim Babangida

Tofa: Hukumar EFCC ta damke Ibrahim Babangida                                                          

Premium Times ta rahoto cewa Hukumar yaki da cin hanci da rashawa watau EFCC ta damke wani mutum mai suna Ibrahim Babangida da laifin zamba. Hukumar ta EFCC dai ta damke takwaran na wani tsohon Shugaban Kasar nan ne dai laifin yin sojar gona, da sata, algushu da kuma hainci.

Hukumar EFCC ta kama wani Ibrahim Babangida
Hukumar EFCC ta kama wani Ibrahim Babangida

 

 

 

 

 

 

Hukumar ta EFCC ta damke Ibrahim Babangida ne tare da wasu abokan aikin sa, masu suna Murtala Mohammed and Nasiru Isa. Abin mamaki kuma dai daya daga cikin su, jami’in Hukumar ne. Nasiru Isa dai, direban Hukumar Yaki da cin Hanci ne na Kasar, ya shiga aikin EFCC kwanakin baya. Hukumar EFCC ta kama sa yana kokarin sace wasu kudi da aka karbo daga wanda suka ci amanar Kasar.

KU KARANTA: Kotu ta cigaba da shari'ar Sanata Kashamu

An kama wani Jami’in dan sanda Kofur Aliyu Ismaila, da tare kuma da Abubakar Jibrin, Abdulsalam Ado, Reuben Dauda, Hassan Aliyu, da Sani Yusuf cikin masu taimakawa Ibrahim Babangida. Abin da dai ya faru shine jami’an EFCC sun yi kokarin kama wasu da ke yunkurin sace wasu kaya da aka karbe, duk suka tsere su ka bar wani kafintada ake ce wa Yakubu Muhammad, wanda Yakubu ne duk ya tina asirin su. An yi amfani da Yakubu wajen damke Isa da kuma Babangida.

Wasu daga cikin ma’aikatan na EFCC ne suka yi kokarin sace wasu kaya da aka karbo daga hannun barayin Kasar nan. An kuwa hada kai ne da Babangida da kuma sauran abokan aikin sa wajen wannan aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel