'Yan Matan Chibok: Kungiyar BBOG bogi ce-Kungiyar Mata

'Yan Matan Chibok: Kungiyar BBOG bogi ce-Kungiyar Mata

Matan Chibok: Kungiyar BBOG bogi ce-Kungiyar Matan Kirista

'Yan Matan Chibok: Kungiyar BBOG bogi ce-Kungiyar Mata
BBOG campaigners are disappointed with the way President Buhari is treating the rescue of the Chibok girls

 

 

 

 

Wata Kungiya ta matan Kirista a Kasar nan ta ware kan ta daga abin da ya shafi sha’anin Kungiyar nan ta BBOG. Kungiyar ta Majalisar matan kirista mai suna WOWICCN, ta bayyana cewa maganar sace ‘Yan matan Chibok da kuma yunkurin ceto su duk yaudarar banza ce kurum. Kungiyar tayi wannan bayani ne a Jiya Juma’a. Jaridar Vanguard ta rahoto Shugaban Kungiyar Rabaraen Omatsola Williams tana cewa abin ya zama son rai.

Omatsola Williams take fada a wani taron Shekara-da-shekara a garin Abuja cewa, yanzu lamarin fafutukar kubutar da ‘yan matan na Chibok ya zama son rai. Matar tana fadin cewa ita ba ta ma yadda akwai wasu ‘Yan mata na Chibok da aka sace ba. Tace ka da a rika amfani da wasu ana rainawa Jama’a hankali, ana kuma samun kudin shiga. Tace fa wasa kawai ake yi da kan mutane, ya ma za ayi ace ba a iya shiga dajin Sambisa?

KU KARANTA: BringBackOurGirs: Gwamna Kashim bai damu da mu ba-Matan Chibok

Shugaban Kungiyar ta WOWICCN tace da aka zo maganar Neja-Delta, ai kowa ya ga zahiri. Amma kuwa maganar Chibok, kawai wasu ne ke wasa da kawunan mu, kuma mata za su dauki mataki. Game da Kungiyar BBOG kuwa, tace ba su da wani amfani. Rabaraen Misis Omatsola tace Kungiyar ta BBOG ba su taimakawa Shugaba Muhammadu Buhari ko ta wace hanya.

Kungiyar dai ta Majalisar matan kirista mai suna WOWICCN tace Kungiyar BBOG #BringBackOurGirls ta su Ezekwesili ta bogi ce kurum!

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng