Shugaba Muhammadu Buhari yazo jihar Katsina

Shugaba Muhammadu Buhari yazo jihar Katsina

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka gida, Daura jahar Katsina ranar juma'a dan yin bikin babbar sallah.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hadu da mai girma gwamnan Katsina Aminu Bello Masari da tsohon gwamnan jahar Katsina Alhaji Sa'idu Barde da mukaddashin gwamnan Katsina Alhaji Mannir Yakubu da mai martaba sarkin Katsina Alhaji Abdulmuminu Usaman Kabir da sauransu a filin tashi da saukar jirage na Umaru Musa Yar'adua.

Shugaba Muhammadu Buhari yazo jihar Katsina
Shugaba Muhammadu Buhari yazo jihar Katsina

A yau dai da rana shugaban kasan ya halacci sallar juma'a gidan gwamnati dake Abuja tare da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da mai bada shawara kan sha'anin tsaro na kasa Babagana Monguno.

Shugaba Muhammadu Buhari yazo jihar Katsina
Shugaba Muhammadu Buhari yazo jihar Katsina

In zaku iya tunawa gwamnatin tarayya ta sanar cewa ranar 12 da 13 na watan satumba a matsayin hutun bikin sallah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng