Jonathan, Atiku, Kalu sunyi makokin Olorogun Micheal Ibru

Jonathan, Atiku, Kalu sunyi makokin Olorogun Micheal Ibru

-Tsohon Shugaban kasa Jonathan, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku da kuma tsohon gwamna Uzor-Kalu, sun yi jimamin mutuwar Olorogun Micheal Ibru

-Jonathan ya bayyana Ibru a matsayin dan kasuwa mai cike da nasara wadda ya taimaka gurin kawo ci gaba a kasuwanci gida

-Atiku yace marigayi Ibru ya kasance mai kiwo, yayinda Kalu yace ya baiwa kasuwanci gagarumin gudunmuwa da ci gaban zamantakewa,tattalin arziki da kuma siyasar Najeriya

Tsohon shugaban kasa Dr Goodluck Ebele Jonathan, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon gwamnan jihar Abia, Dr. Orji Kalu, a jiya 8 ga watan Satumba, sun nuna bakin cikinsu kan mutuwar Olorogun Micheal Ibru.

Su ukun sun girmama marigayi Ibru wanda ya mutu a makon nan yana da shekaru 85 a duniya.

Jonathan, Atiku, Kalu sunyi makokin Olorogun Micheal Ibru
Michael Ibru ya mutu yana da shekaru 85

Yayinda Jonathan ya bayyana shi a matsayin dan kasuwa mai nasara wanda ya bada gudunmuwa ga kananan sana’a a kasar, Atiku yace marigayi Ibru mai kiwo ne wanda yay i imanin cewa kasuwancin kasa zai iya yin fice kuma harma yayi gasa na kasashen waje.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta shirya daukar masu digiri 100,000 aiki

A bangarensa, Kalu yace Ibru ya bada gagarumin gudunmuwa gurin ganin ci gaban Najeriya ta hanyan zamantakewa, tattalin arziki da kuma siyasa, jaridar The Sun ta ruwaito.

Ya bayyana cewa marigayi dan kasuwan ya taimaka wa rayuwar mutane da dama ta hanyar daular kasuwancin sa.

Kalu ya bukaci gwamnatin jihar Delta da ta daukaka marigayi dattijon jihar ta hanyar sanya sunan sa a wani gaggarumin aiki, yayinda yake ta’aziya tare da al’umman Urhobo.

Tsohon gwamnan ya kallafa wa iyalan Ibru da su riqi kyawawan halaye irin na marigayi, ya kara da cewa za’a dunga tuna kasuwancin marigayi saboda ya samar da ayyukan yi da kuma arziki ga mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: