Yadda ‘yan majalisun Najeriya ke cin kudi

Yadda ‘yan majalisun Najeriya ke cin kudi

– Najeriya ta samu karayar tattalin arziki

– Sai dai yayin da Kasar Najeriya ke fama da durkushewar tattalin arziki, ‘yan Majalisun kasar ba bin da suke yi sai cin kudi

– Duk duniya dai Najeriya na cikin kasashen da ‘yan Majalisu ke karbar albashi karbar hauka

Yadda ‘yan majalisun Najeriya ke cin kudi

Yayin da ake fama da karayar tattallin arziki a Najeriya, ‘Yan Majalisu su kuwa karen su suke ci babu babbaka!

Wani bincike da Hukumar yaki da cin hanci da rashawar Kasar ta gudanar ya nuna cewa ‘Yan Majalisar Kasar nan suna tashi da akalla abin da ya fi Naira biliyan 6 a kowace shekara. ‘Yan Majalisun sun hada da Majalisar wakilai da kuma ra dattawar Kasar. A cikin shekara guda suna karbar abin da ya kai N6.78b. Kuma dai, an saba samun Majalisar da yin awon-gaba da wasu kudin.

Wata Jarida ta bayyana kudin da ‘yan majalisun Kasar nan suke karba a shekara. An samu wannan bayani ne daga ofishin da ke kula da rabon albashin Kasar; ‘Revenue Mobilisation, Allocation and Fiscal Commission’ Watau RMAFC. Alawus da albashin ‘yan Majalisun ya kai Naira Biliyan shida. Alawus din dai sun hada da na karshen shekara, gida, na mai da kuma na mota, na mataimaka, gyaran gida da masu aikin gidan, dawainiya, gyaran mota, da kuma na jin dadi. Akwai dai wasu alawus din da suka hada har da su na sutura, na jaridu, na tafiye-tafiye, da nah utu, na dawainiya da kuma na mazaba, har da ma dai alawus din wahala.

KU KARANTA: An sace ma'aikatan Mai a jihar Rivers

Albashin Shugaban Majalisar dattawa ya kai N2.48m inda kuma mataimakin sa ke karbar N2.30, Shugaban Majalisar wakilai kuwa na karbar N2.47, mataimakin sa kuwa na yin gaba da N2.28 a kowace shekara. Albashin dukkanin Majalisar dattawan a shekara ya kai Naira biliyan 1.85, inda kuma ‘yan uwan aikin na su har su 360 ke tashi da Naira Biliyan 4.93.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng