Garkuwa da mutane: An sace 14 a jihar Ribas
1 - tsawon mintuna
'Yan sanda a Najeriya sun ce an sace wasu ma'aikatan kamfanin mai su goma sha hudu da direbansu a jihar Rivers dake kudancin kasar.
'Yan sandan sun ce wasu 'yan bindiga ne suka tare motar da ma'aikatan ke tafiya a cikinta akan hanyarsu ta zuwa aiki a Fatakwal babban birnin jihar.
Daga baya ne aka gano motar ta su da aka yasar.
'Yan sandan sun ce suna ci gaba da bincike a cikin daji da cikin ruwa, amma har yanzu ba su san ko su wanene suka sace mutanen ba.
Garkuwa da mutane don neman kudin fansa ya zama ruwan dare a yankuna masu arzikin mai a Najeriya.
Mutanen da ake sacewar sun hada da attajirai 'yan kasar da kuma baki 'yan kasashen waje.
Asali: Legit.ng
Tags: