Ku zo mu hada hannu tare mu yaki ciwon yunwa- Aisha Buhari
Aisha Buhari ta kaddamar da yakin nenman zabe mai taken “ku shiga ciki” a matsayin daya daga cikin shirin ta na nan gaba da ta zata shirya domin kawo mafita ga matsar ciwon yunwa dake addabar yara kanana.
Matar Shugaban kasa Aisha Muhammadu Buhari ta kaddamar da ka sance a ciki “get involved” a matsayin shirin ta na nan gaba a ranar 29 ga watan Afrilu na shekara 2016
Taron ya samu halartan Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari da matayen gwamnonin sauran jihohi kamar jihar Kebbi, Sakwato, Borno, Nassarawa, Plateau da Niger
Matar Shugaban kasar Najeriya ta yi imanin cewa himmar ta zai jawo hankalin masu tunani, wakilan kafanonin kai ba da kuma kungiyoyin da ba na gwamnati ba domin magance ciwon yunwa da ke addabar yan gudun hijira.
KU KARANTA KUMA: Mai tafiya aikin hajji tayi kashin hodar iblis kunshin 76
Yau ne rana na biyar na taron wanda ya samu halartan Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari da matayen gwamnonin sauran jihohi kamar jihar Kebbi, Sakwato, Borno, Nassarawa, Plateau da Niger.
Bisa ga sabon rahoton da kungiyar UNICEF tayi a kwanan nan, sama da jariran Najeriya miliyan 5 aka Haifa da ciwon yunwa.
KU KARANTA KUMA: Afenifere, Ohanaeze sun kai hari ga Abdullahi
A halin yanzu, an kididige kimanin kwatan yaran jihar Borno na fuskantar matsanancin ciwon yunwa da kuma barazanar mutuwa, sakamakon rikicin da kungiyar Boko Haram suka haddasa a jihar.
Asali: Legit.ng