Mai tafiya aikin hajji tayi kashin hodar iblis kunshin 76
-Hukumar NDLEA sun kama wata mace a hanyarta na zuwa kasar Saudiya tare da kunshin hodar iblis 76 bayan tayi kashi
-Matar da aka kama tace ta hadiyi kwayoyin hodar iblis din ne saboda ta bunkasa kasuwancinta na kayan kwaliyya daga cikin abunda zata samu idan ta siyar da hodar iblis din
-An kama matar mai shekaru 55 a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe a cikin jirgin kasar waje a ranar Juma’a, 2 ga watan Satumba
Hukumar dake kula da masu sakafar mugayen kwayoyi wato National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA) sun bada wata sanarwan cewa anyi wa wata Yar kasar Najeriya da zata tafi birnin Madina, Kasar Saudiya, domin tayi aikin hajji, gwajin kwayoyi kuma ya nuna tana dauke da shi, a ranar Juma’a, 2 ga watan Satumba, a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe, Abuja.
Matar mai suna Basira Binuyo tana da shekaru 55 a duniya.
KU KARANTA KUMA: Matasan Enugu sunki amincewa da kai hari ga makiyaya
An cafke Binuyo a yayinda ake binkikar mahajata a cikin wani jirgin kasar waje da zai tafi birnin Madina ta kasar Dubai, babban birnin larabawa (UAE)
Hamisu Lawan, kwamandan hukumar NDLEA dake filin jirgin saman Abuja ya bayyana cewa “ zuwa yanzu tayi kashin miyagun kwayoyi 76 wanda aka gwada ya kuma yi daidai da hodar iblis.
“A halin yanzu, tana karkashin kulawa har sai anyi nasarar fito da dukkan miyagun kwayoyin.”
Mai safarar miyagun kwayoyin asalain yar karamar hukumar Irepodun dake jihar Kwara, tsakiyar arewacin Najeriya tana kuma da aure da yara uku. An ce yar kasuwace a kasuwar Dosumu, jihar Lagas.
A lokacin da take bayani kan abunda tayi. Binuyo tace yunkurinta na bunkasa kasuwancinta ne ya kaita ga aikata laifin.
Irin wannan mumunan al’amarin ne ya faru kimanin makwanni uku da suka wuce, lokacin da aka kama yan Najeriya uku daga jihar Kwara kasar Saudiya kan shiga da hodar iblis kasar.
Asali: Legit.ng