Labarai guda 9 da sukayi fice a ranar Juma’a

Labarai guda 9 da sukayi fice a ranar Juma’a

Tawagar Legit.ng sun harhado maku muhimman labarai da sukayi fice a kannan labaran ranar Juma’a, 2 ga watan Satumba. Ku nemi dukkan labaran da kuka rasa a kasa.

1. A yanzu haka: Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana yawan kudin da aka samu daga masu cin amanar kasa.

Minista Lai Mohammed ya bayyana cewa kasar Najeriya ta dawo da kimanin naira biliyan 78, da kuma dala miliyan 3 daga masu cin amanar kasa tunda aka rantsar da Muhammadu Buhari.

2. An bayyana Yan Najeriya 5 wanda mutuwarsu zai halaka Najeriya. Zaman lafiyar Najeriya na cikin matsanacin hali kuma abunda zamu iya cewa shine Allah ya shige mana gaba a kan komai, kaddarar kasar nan ya ta’allaka hannun wasu mutane.

Labarai guda 9 da sukayi fice a ranar Juma’a
Shugaba Muhammadu Buhari da Shugaban Sojojin Najeriya, Tukur Buratai

KU KARANTA KUMA: Najeriya ka iya kamuwa da cutar Zika- bincike

3. Gara an kirani da shege da a kirani danka- babban dan Oduah yace ma mahaifinsa. Bayan sanarwan Satchie Etoromi, tsohon mijin Sanata Stella Oduah, daya daga cikin yaransu, Tuoyo Etoromi Oduah, ya bayyana wani tsinannan sanarwa ga mahaifin sa.

4. Abun al’ajabi! An gano zinari a jihar arewacin Najeriya, Wani mai amfani da shafin sadarwa na Facebook, Jaafar Jaafar ya yada wani rubutun wani abokinsa Rufa’I Dabo, wadda yayi rubutu mai dadi bayan ya ziyarci karamar hukumar Bagwai da Shanono a jihar Kano.

Labarai guda 9 da sukayi fice a ranar Juma’a

5. Abun kunya! An dakatar da wani Ministan kasar India, Sandeep Kumar, bayan an yada wani faifai bidiyo da ya nuna shi yana sumbatar mata biyu a kafofin watsa labarai.

Labarai guda 9 da sukayi fice a ranar Juma’a

KU KARANTA KUMA: Matasan Enugu sunki amincewa da kai hari ga makiyaya

6. Shugaban kasa Muhammadu Buhari yaba yan Najeriya tabbacin cewa Chanjin da gwamnatin sa tayi alkawari zai wakana bayan kokari, hakuri da juriya.

7. Wa ya san cewa tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soja, Sani Abacha, nada wadannan kyawawan jikoki. An nuno hotunan su suna shakatawa a kasar Dubai.

Labarai guda 9 da sukayi fice a ranar Juma’a
Jikokin Abacha

Asali: Legit.ng

Online view pixel