Shahararren yayi bikin cikan aurensa shekaru 15

Shahararren yayi bikin cikan aurensa shekaru 15

Fitaccen dan wasan barkwanci Okechukwu Anthony Onyegbule da aka fi sani Oke-Bakassi tare da matarsa Zizi sunyi bikin cikan aurensu shekaru 15 a ranar 1 ga watan Satumba.

Shahararren yayi bikin cikan aurensa shekaru 15
Okey da Zizi

Okey ya daura hotunan murnan nasu ne a shafinsa na Instagram inda yayi musu taken “lokaci na gudu, nayi mamaki wai har mun shafe shekaru 15 da aure. Tun bayan da ni da matata muka yanke shawarar zama tare da juna da soyayya, abin sai dai godiya.

“Munyi rashin iyayen mu, amma mun sama musu jikoki guda uku. Don haka nake ma matata Zizi godiya da irin kulawar da take ma iyalinmu, ni kuma zanyi iya bakin kokarina inga na faranta miki rai.

“Murnan zagoyar ranar aurenmu zuwa ga iyalan Onyegbule gaba daya.”

Shahararren yayi bikin cikan aurensa shekaru 15
Okey da Iyalinsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel