Messi ya koma Argentina

Messi ya koma Argentina

Jagoran yan wasan Ajantina Lionel Messi ya zura kwallo a wasan da suka fafata da kasar Uruaguay, wannan shi ne wasan shi na farko tun bayan ya janye murabus din da yayi.

Messi ya koma Argentina

Wasan da kasashen biyu suka gwabza wasan neman cancantar shiga gasan cin kofin duniya ne, inda Ajantina ta lallasa Uruguay 1-0 ta hannun Lionel Messi wanda ya zura kwallon gab da tafiya hutun rabin lokaci, hakan ya baiwa sabon kocin Ajantina Edgardo Bauza nasarar sat a farko a matsayin sa na kocin Ajantina.

Duk da cewa Ajantina sun rasa dan wasa daya, bayan an sallami Paulo Dyabla sakamakon aikata laifi bayan an dawo hutun rabin lokaci, amma Ajantina sun rike wasan yadda ya kamata.

Messi ya koma Argentina

A baya dai Messi yayi murabus daga yi ma Ajantina wasa bayan sun samu rashin nasara a hannun kasar Chile a wasan karshe na gasan cin kofin nahiyar Amurka a watan yulio, sai dai Messi ya janye murabus din da yayi bayan al’ummar kasar sun bashi hakuri.

A yanzu dai Ajantina sune a saman jadawalin kasashen dake fafatawa a gasar, suna saman Uruguay, Ecuador da Columbia bayan wasannin bakwai.

A wani labarin kuma, Neymar ya zura kwallo daya inda Gabriel ma ya zura kwallaye biyu a wasan da suka gwabza da kasar Ecuador, wanda hakan ya zamto nasara ta farko da sabon mai horar dasu Tite ya samu.

Messi ya koma Argentina
Yan wasan Brazil suna taya Neymar murna

A yanzu dai Brazil ita ce ta 5 a jerin kasashen, kuma zata buga wasan ta na gaba da Columbia.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel