Manyan labarai a ranar Alhamis
Jaridar Legit.ng ta tattara manyan labarun da aka samu ranan Alhamis,1 ga watan Satumba
1. Buhari ya bada umurnin titin jirgin kasan Legas-Kano ya bi ta jihar Ekiti
Shugaba buhari ya bada umurnin cewa titin jirgin kasan da za'a yi na Legas zuwa kano ya bi ta ekiti.
2. Apostle Chukwusom Okoli ya ce yan kabilar igbo masu bautan shaidan ne
Apostle Chukwusom Okoli ya kalubalanci mayu da bokaye da suyi fito na fito da shi
3. Shekau ya mutu - Hukumar Sojin Kasa
Rundunar sojin kasan najeriya sun sake alanta cewa sun kashe shugaban bok haram Abubakr shekau .Kwamandan operation lafiya dole, Janar Lucky Irabor,ya ce shugaban kungiyar boko haram, Abubakr shekau ya mutu
4. An canza ranar komawan dalibai makaranta
Ministan babban birnin tarayya, Muhammad Bello ya amince da canza ranar komawar daliban firamare da sakandare makaranta. Ya bayyana hakane a wata jawabi a ranan laraba, 31 ga watan agusta.
5. Yan bindigan Neja delta sun sake kai hati, kuma suna ma Okorocha barazana
KungiyarNiger Delta Red Squad (RDRS), sun sake kai wani mumunan hati bututun man Kamfanin Agip da ke Umuonei da ke Awara a jihar Imo.
6. PDP ta mutu a jihar Edo - Oyegun
Shugaban jam'yyar APC ta kasa,Cif John Odegie-Oyegun ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ta mutu a jihar sanadiyar shekewan mambobinta 3000 zuwa APC.
Asali: Legit.ng