Kelechi Nwakali ya bar Arsenal
– An karbi aron dan wasa Kelechi Nwakali daga Arsenal
– Dan wasan zai bugawa Kungiyar MVV Maastricht
– Dama can Nwakali bai taba bugawa Arsenal wasa ko daya ba.
An karbi aron dan wasan Najeriyar nan da ke Kungiyar Arsenal watau Kelechi Nwakali. Yanzu haka dan wasan zai koma wata karamar Kungiya mai suna MVV Maastricht da ke kasar Holland.
KU KARANTA: Allardyce ya yabi Jay-Jay Okocha
Arsenal ta bada aron dan wasan ta na Kasar Najeriyar nan, Kelechi Nwakali. Dan wasan zai bugawa Kungiyar MVV Maastricht aro shekarar nan. Sabuwar Kungiyar dan wasan dai tana Kasar Holland ne na Turai, inda ta ke buga mataki na biyu na Gasar Kasar.
Dan wasa Kelechi Nwakali ne ya karbi kyautar wanda ya fi kowa iya kwallo a Gasar Kofin duniya na masu kasa da shekaru 16 watau U-17 World Cup da aka buga shekaru biyu da suka wuce. An dai buga wannan gasa ne da Nwakali yayi kaurin suna ne a Kasar Chile a shekarar 2015, inda har aka bas a kyautar takalmin gwal.
Dan wasan yana da shekaru 18 a duniya, kuma yana buga gurbin tsakiya. Ya dai koma Kungiyar ta Arsenal ne daga wata Makaranta ta horar da ‘yan wasa mai suna ‘Diamond youth academy’ cikin wannan shekarar, sai dai bait aba bugawa Kungiyar Arsenal din ba, musamman a wani babban wasa.
Kocin Kungiyar MVV Maastricht, Ron Elsen na san ran cewa dan wasa Nwakali zai samu buga wasanni a Kungiyar ta sa, kafin ya komo Gidan Emirates na Kungiyar Arsenal.
Asali: Legit.ng