Balotelli ya koma Kungiyar Nice

Balotelli ya koma Kungiyar Nice

– Kungiyar Liverpool ta katse kwantiragin dan wasa Mario Balotelli

– Yanzu dai dan wasan ya koma Kungiyar Nice na din-din-din, babu ko sisin-kobo

– A shekarar 2014 Kocin Liverpool na lokacin, Brendan Rodgers ya sayi dan wasa Balotelli

Balotelli ya koma Kungiyar Nice

Kungiyar Liverpool ta katse kwantiragin dan wasa Mario Balotelli ta kuma sanar da cewa dan kwallon ya koma Kungiyar Nice.

Liverpool ta tabbatar da cewa dan wasa Mario Balotelli ya bar Kungiyar zuwa wani Kulob da ake kira Nice a Kasar Faransa. Liverpool dai ta katse kwantiragin dan wasan ne, hakan ta sa ya koma Kungiyar Nice ba tare da sisin-kobo ba. Balotelli dai yanzu zai bugawa Kungiyar Nice da ke Kasar Faransa.

Rayuwar Dan wasan nan na Kasar Italiya, Mario Balotelli ya zo karshe a Kungiyar Liverpool ta Ingila, bayan ya shafe shekaru biyu ana ta kai ruwa rana, dan wasan ya koma Kungiyar Nice da ke Faransa na din-din-din. Duk da cewa akwai saura shekara guda da ta rage daga kwantiragin dan wasan da Kungiyar Liverpool, Kocin Kungiyar, Jurgen Klopp ya bayyana cewa ba ya bukatar dan wasan. Dalilin wannan ya sa Kungiyar ta katse kwantiragin na sa, hakan ta sa dai dan wasan ya bar Kungiyar.

KU KARANTA: JOE HART YA TASHI DAGA MAN CITY

Shekaru biyu da suka wuce, Kocin Liverpool a wancan lokaci, Brendan Rodgers ya sayo dan wasan, sai dai tun zuwan sa, kwalla daya tak yaci a Gasar Premier League. Bayan nan ne Kungiyar AC Milan ta karbi aron tsohon dan wasan na ta.

Sai ga shi wannan shekarar dan wasa Mario Balotelli ya dawo Kungiyar Liverpool din, sai dai Kocin Kungiyar Juegen Klopp, ya nuna alamun cewa ba zai yi da dan wasan ba, don kuwa ba da shi aka buga duk wasannin sharan fagen Kungiyar ba a Kasar Amurka, wasanni har kusan goma.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel