Super Eagles ba su da alawus ko sun doke Tanzania

Super Eagles ba su da alawus ko sun doke Tanzania

– Ba za a ba ‘Yan wasan Super Eagles wani alawus ba ko da sun buge Kasar Tanzania

– Kungiyar kwallon kafar Najeriyar za ta kara da Kasar Tanzania a wasan zuwa Gasar Kofin Nahiyar Afrika na 2017

– Sai duka Kasashen ba za su sami zuwa Gasar ba, wanda za ayi badi

Super Eagles ba su da alawus ko sun doke Tanzania

Shugaban Hukumar kwallon kafar Najeriya (NFF) Amaju Pinnick yace ‘yan wasan Najeriya ba su da alawus ko da sun doke Tanzania.

Shugaban Hukumar kwallon kafar Najeriya (NFF) Amaju Pinnick ya bayyana cewa ‘Yan wasa da jami’an Super Eagles na Najeriya ba za su samu wasu alawus ba idan sun buge Kasar Tanzania a wasan zuwa Gasar cin Kofin Nahiyar Afrika da za su buga a Ranar Asabar mai zuwa.

Shugaban Kungiyar ta NFF, Pinnick, yace Hukumar NFF ta Kasa ba ta da Kudin da za ta rabawa ‘yan wasan Kungiyar, kuma ma asali dai babu amfanin hakan, tun da Kasar ba za taje Gasar Nahiyar ba a shekara mai zuwa. Shugaban Hukumar ya kuma bayyana cewa ba za a iya ba ‘yan wasan wasu kudi ba a yanzu har sai gwamnati ta fitar da su.

KU KARANTA:  An dauki aron dan wasan Najeriya Omeruo

Amaju Pinnick yana mai ce da Jaridar CompleteSports: “Dole ‘yan wasa su kara hakuri da mu, domin kuwa yanzu babu kudi, amma idan har an samu kudin za mu biya kowa” Pinnick ya bayyana cewa ana cikin wani hali ne. Ko a yanzu haka, Gwamnatin Jihar Akwa-Ibom ne ta dauki nauyin masaukin ‘yan Kungiyar Super Eagles din. Pinnick yace: “Da mun shiga cikin matsala babba, idan har da Gwamnatin Jihar Akwa-Ibom ba ta bamu masauki ba, su suka dauki nauyin kudin otel din mu, wanda ya kai Naira Miliyan 50. Da ba mu san inda za mu samu biyan wannan kudin ba!”

Kungiyar Super Eagles za ta buga wasan zuwa Gasar ‘Africa Cup of Nations’ da Kasar Tanzania a ranar Asabar.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel