Ku daina ganin laifi na - Dalung

Ku daina ganin laifi na - Dalung

– Solomon Dalung yace ba fa bayan zuwan sa Minista bane aka fara samun matsaloli a sha’anin wasannin Najeriya

– Ministan yace an yi kuskure da aka soke Hukumar kula da wasannin Kasar watau ‘Nigerian Sports Commission

– Dalung yace dole sai anyi gyara wajen sha’anin wasanni a kasar

Ku daina ganin laifi na - Dalung

Ministan wasannin na Najeriya Solomon Dalung, yace a daina ganin laifin sa don ba yau Najeriya ta fara samun matsaloli ba a harkar wasanni.

Minista Dalung yayi kira ga masu sukar sa su san da cewa fa tun kafin ya zama Minista ake fama da matsaloli a harkar wasannin Najeriya. Ministan yayi wannan jawabi ne a Ranar Talata bayan y agama tattaunawa da Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari a game da sha’anin wasannin Olympics. Najeriya dai ta samu kyautar tagulla, bayan ta zo na uku a gasar.

KU KARANTA: Kungiyar Chelsea ta bada aron Kenneth Omeruo

Minista Dalung yave ba fa shine matsalar ba ko kadan, don tun kafin ya zo Najeriya ba ta taka wani rawar gani. ‘Wasu Yan Najeriyar suna ganin ya kamata ace an kori Ministan saboda sakamakon Kasar a Gasar RIO Olympics na wannan shekarar, duk da cewa bai wuce shekara guda ba da aka nada sa.

Ministan wasannin Kasar, Dalung yayi kira da cewa doke a koma asali, domin a ga inda matsalar ta ke, haka kuma yace bai dace ace an soke Hukumar kula da wasannin Kasar ba watau ‘Nigerian Sports Commission’.

A bayan nan dai Ministan ya kira Hukumar Kwallon kafar Kasar (NFF) da ta taimaka ta biya Kocin Kungiyar U-23 na Kasar, Samson Siasia albashin sa da yake bi bashi. Ministan yayi wannan roko ne lokacin da Kocin da kuma matar Sa, Misis Eunice Siaisia suka ziyarce sa. Ministan ya kira Sakataren Hukumar NFF din Dr Mohammed Sanusi, da su taimaka su biya mai horar da ‘yan wasan kudin sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel