Super Eagles ta lallasa kungiyar Premier League a wasar gwaji

Super Eagles ta lallasa kungiyar Premier League a wasar gwaji

- Super Eagles sun lallasa Akwa United a wasar gwaji a Uyo

- Nosa Igiebor da Odion Ighalo duk sun jefa kwallo

- Wannan ita ce wasar gwaji ta farko da Gernot Rohr a matsayin mai horarwa

Super Eagles sun lallasa kungiyar Akwa United da ci 3-0 a wasar sa da zumunci wanda aka doka a filin wasa na Akpabio ranar Laraba da yamma.

Brown Ideye, Nosa Igiebor da Odion Ighalo su suka jefa kwallayen yayin wasar da Akwa United.

Super Eagles ta lallasa kungiyar Premier League a wasar gwaji
Super Eagles

Mintuna 28 Ideye ya jefa kwallo daya jaws tun daga baya, sai wanda ya dawo daga kungiyar daga baya Igiebor ya jefa kwallo ta 2 a mintuna na 39.

Ighalo da aka sawo bayan hutun rabin lokaci yaci da finariti lokacin da Sabon dan wasan Akwa United yayi keta aka bashi doruwan kati na 2 inda ya fita filin.

Super Eagle zasu yi wasa ranar Asabar, wasar share fage zuwa cin kofin nahiyar bakake wanda zasu doka da Tanzania.

Asali: Legit.ng

Online view pixel