Jami’in soja ya bayyana sirrin Boko Haram

Jami’in soja ya bayyana sirrin Boko Haram

Wani babban jami’in rundunar sojan kasar nan Manjo janar Lucky Irabor yace ana sa ran rundunar zata kwace sauran yankunan kasar nan dake karkashin kungiyar yan ta’adda ta Bokoharam a yan satuttuka kadan masu zuwa.

Jami’in soja ya bayyana sirrin Boko Haram
Manjo Janar Irabor

Irabo, wanda shi ne kwamanda hakkin rugurguza yan bokoharam ya rataya a wuyarsa ya bayyana hakan ne a ranar laraba 31 ga watan agusta.

Rundunar sojan ta gaza cimma kammala yakar yan Bokoharam a watan Disambar bara kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ayyana, a baya dai Bokoharam tayi kokarin kafa daular musulunci a yankunan tafkin Chadi, wanda ya kai girman fadin kasar Belgium, amma rundunar sojin Najeriya ta kwato da dama daga cikin yankunan.

Kwamandan yaki Irabor yace a yanzu haka yan Bokoharam na buya ne a wasu yankuna kadan na dajin Sambisa inda yan mata fiye da 200 suke kame yan makarantar Chibok tun shekarar 2014, kuma ana zaton kungiyar na kame da yaran ne a tsakan kanin tafkin Chadi, inda ya kara dacewa nan bada dadewa ba zasu kwato yaran.

Duk da irin kayin da take sha, Bokoharam ta cigaba da gudanar da kunan bakin wake a wasu sassan kasar nan, Kamaru, Nijar da Chadi. An kashe mutane sama da 15,000 tun a shekarar 2009 da aka fara yaki da Bokoharam, inda sama da mutane miliyan 2 suka shiga gudun hijira wanda yayi sanadiyyar karyewar tattalin arzikin jama’an yankin.

“Kusan duk yankunan dake karkashin bokoharam mun kwato su, abinda yayi saura kawai sune wasu yan kauyuka da garuruwa kadan ne suka rage.” Inji Irabor a wata hirar da yayi da yan jarida a birnin Maiduguri.

Yawancin nasarar da aka samu kan Bokoharam ya samu ne ta hanyar aikin hadin gwiwa da ake yi tsakanin Najeriya da makwabtan kasashen ta, musamman kasar Chadi wanda sojojinta k eta kashe yan bokoharam a yayin da suke kokarin tsallakawa kasar don neman tsira.

“Aikin hadin gwiwa muke yi. Kwamandoji na sun shirya da kwamandojin makwabciyar mu, sakamakon haka ya sanya yan bokoharam shiga tsaka mai wuya, a yan satuttuka kadan zaku ji labara mai dadi.” Inji shi.

Yace yan bangaren  bokoharam da suka yi mubaya’a ga kungiyar ISIS a bara, sune masu rike da garuruwan Abadan da Malafatori duk a gaban tafkin Chadi baya da sansanin su dake cikin dajin Sambisa dake kudancin Maiduguri. Yace a yanzu rundunar soja na shirin kai wani samame na musamman cikin dajin Sambisa bayan sun dakatar da gudanar da hakan sakamakon mamakon ruwa da ake zabgawa a garin.

“Mun gudanar da wani samame a dajin Sambisa a farkon shekarar nan, mun samu nasara, amma yanayin dajin ya sanya dole muka ja da baya sakamakon ruwa da ake yi.” Yace rundunar sojan ta ceto sama da mutane 20,000 daga hannun yan bokoharam cikin mutane sama da miliyan 2 da hukumar kula da yara ta majalisar dinkin duniya ta bayyana suna tsare a yankin tafkin Chadi.

Game da mutuwar shekau

Sansanin manjo janar Irabor na gefen garin Maiduguri ne, da ganinsa kasan hakan ya nuna irin kyakkyawan canjin da shugaban kasa Buhari ya kawo ma sojojin kasar nan ne, saboda irin dakuna da gidajen da aka gina ma sojoji a sansanin.

A zamanin baya kuwa Sojoji sun yi korafin rashin kayan aiki, don haka suka yi kaurin suna wajen guduwa daga bakin daga hare haren yan bokoharam. A yan kwanakin da suka gabata ne kasar Birtaniya da wasu manyan kasashen duniya suka kara yawan tallafin da suke yi ma rundunar sojojin kasar nan. a watan Mayu, jami’an kasar Amurka da ta hana sayar ma Najeriya makami sun shaida ma kamfanin Reuters cewa a yanzu zata siyar ma najeriya da wasu jiragen sama na yaki, majalisar kasar ake jira su bada izinin cinikin a yanzu.

Sa’annan Irabor ya bude teburin sauraron koke koken cin zarafin dan adam, “dokan aiki a fayyace yake ga kowa, muna daukan maganan cin zarafin dan adam da muhimmanci sosai” in ji shi.

Irabora ya kara da cewa sun jikkata shugaban kungiyar Bokoharam Abubakar Shekau a yanzu haka, inda ya janye batun da rundunar sojan sama tayi tana cewa wait a kashe shi. “mun jikkata Shekau, wannan shi ne tabbacin magana, amma zance ko ya mutu ko bai mutu ba, ba zan iya tabbatarwa ba a yanzu.”

Tun sa’ilin da labarin jikkata Shekau ya bayyana, kungiyar bokoharam bata ce komai ba, hatta fitar da sanarwa da take yi a shafin yanar gizo, duka bata yi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel