Dan wasan Arsenal ya koma Werder Bremen a ranar karshe

Dan wasan Arsenal ya koma Werder Bremen a ranar karshe

Dan wasan Arsenal, Serge Gnabry, ya koma Werder Bremen da murza-leda, sai dai ba a bayyana kudin da aka sayi dan kwallon ba.

Dan wasan tawagar Jamus, ya ci kwallaye shida a gasar Olympic da aka yi a birinin Rio, inda Brazil ta ci Jamus a wasan karshe.

Gnabry mai shekara 21, ya koma Arsenal a shekarar 2011, ya kuma buga mata wasanni 18, inda ya ci kwallo daya.

Rahotanni da aka wallafa a ranar Talata sun ce dan kwallon zai koma Bayern Munich da taka-leda ne, daga baya aka ji shi a Bremen.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel