Schweinsteiger ya yi wa kasar sa Jamus wasan karshe

Schweinsteiger ya yi wa kasar sa Jamus wasan karshe

Kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Jamus, Bastian Schweinsteiger, ya buga wa kasar wasan karshe a ranar Laraba.

Schweinsteiger mai shekara 32, ya sharbi kuka lokacin da ake gabatar da shi gaban 'yan kallo a wasan sada zumunta da Jamus ta ci Finland 2-0.

Dan wasan Manchester United, ya fara yi wa Jamus tamaula a watan Yunin 2004, ya kuma buga wa kasar wasanni 121, inda ya ci kwallaye 24.

Schweinsteiger shi ne dan wasan Jamus da ya fi yawan buga wa kasar gasar cin kofin nahiyar Turai, inda ya yi wasanni 18, yana kuma cikin 'yan wasan da suka ci wa kasar kofin duniya a shekarar 2014.

Asali: Legit.ng

Online view pixel