Nasri ya koma kungiyar Sevilla
1 - tsawon mintuna
Dan kwallon Manchester City, Samir Nasri, ya koma Sevilla da taka leda aro.
Dan wasan Faransa ya bar City duk da ya buga mata gasar Premier da ta ci West Ham United 3-1 a ranar Lahadi. Pep Guardiola bai bar Nasri ya yi atisaye tare da 'yan wasa ba, bayan da ya dawo daga hutu, sakamakon teba da ya kara yi.
Mai tsaron ragar City, Joe Hart da Wilfred Bony sun koma wasu kungiyoyin domin buga wasa aro.
Asali: Legit.ng