Yan sanda sun mamaye sakatariyar APC na jihar Ondo

Yan sanda sun mamaye sakatariyar APC na jihar Ondo

- Jami’an yan sandan Najeriya sun mamaye sakatariyar jam’iyyar All Progressive Congress (APC) babin jihar Ondo

- Yan sanda sunce han kai jami’ai sakatariyar APC domin hana karya doka daga wasu mambobi da wadanda ba mambobin jam’iyyar ba

- Shugaban jam’iyyar na jihar ya kuma ba da tabbacin cewa za’a gudanar da zaben zango na farko cikin lumana a ranar Asabar

Yan sanda sun mamaye sakatariyar APC na jihar Ondo
Shugaban jam'iyyar APC ta kasa baki daya, John Odigie-Oyegun

Jami’an Yan sandan Najeriya sun mamaye sakatariyar jam’iyyar ALL Progressive Congress (APC) babin jihar Ondo.

Bisa ga rahoto daga jaridar Daily Sun, jami’in dan sanda dake kula da dangantakar jama’a (PPRO), Mr Femi Joseph yace an kai jami’an yan sanda sakatariyar domin su hana karya doka daga mambobi da wadanda ba mambobin jam’iyyar ba.

KU KARANTA KUMA: Fulani makiyaya sun kai hari ga Fayose kan dokar kiwon dabbobi

“Mutanen mu na gurin kuma zasu ci gaba da kasancewa a gurin har sai zaman lafiya ya dawo jam’iyyar. Bama son mutanen mu suyi amfani da wannan daman sabanin da ya shiga tsakanin yan jam’iyyar su tada rigima a jihar, saboda haka mun rigada mun bayyana dalilin da yasa mutanen mu suka kasance a gurin” Cewar sa.

Rahoton ya kara da cewa an dauke kayan asirin da aka ajiye a kofar shiga sakatariyar, yayinda sakatariyar jam’iyyar ta kasa baki daya suka sanya baki cikin rikicin.

KU KARANTA KUMA: Malami ya ba dalibinsa kyauta

A halin yanzu, shugaban jam’iyyar na jihar ya ba da tabbacin cewa zasu gudanar da zaben zango na farko cikin lumana a ranar Asabar.

Jam’iyyar ta kuma karyata labaran cewa ta cire shugaban ta, Hon Isacc Kekemeke, cewa jam’iyyar na karkashin kulawar Kekemeke kuma zai ci gaba da kasancewa haka har sai sakatariyar jam’iyyar ta kasa baki daya ta yanke shawara da ya saba da haka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel