Jam’iyyar PDP ta mutu a jihar Edo
- Cif John Odegie-Oyegun ya amshi mambobin jam’iyyar PDP da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC
- Shugaban jam’iyyar APC yace har yanzu akwai gurin saukar wasu masu sauya sheka (wadanda zasu dawo jam’iyyar)
- Ya bayyana cewa jam’iyyar PDP yam utu a jihar Edo
Cif John Odigie-Oyegun ya bayyana cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP ta mutu bayan mambobin jam’iyyar da dama sun sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressive Congress (APC).
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Oyegun yayi wannan furucin ne lokacin da ya tarbi shugabannin jam’iyyar PDP sama da dubu uku (3000) zuwa jam’iyyar APC a karamar hukumar Oredo dake jihar Edo.
KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun sace mutane uku a jihar Lagas
Wasu daga cikin manyan mambobin jam’iyyar PDP da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC sun hada da, Mr. Ebima Ogbeide, Tony Anileh, Madam Goldenpenny, Pius Izemwingie, Ikponmwonsa Usiobafoh, Mrs. Vero Aguebor, Wilfred Enabulele, secretary ward 5, da kuma Mr. Ebima Ogbeide.
Shugaban jam’iyyar ta APC yace har yanzu jam’iyyar a shirye take ta tarbi mambobin jam’iyyar PDP ko guda nawa ne da suke da sha’awar barin jam’iyyar.
Har ila yau, Gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole ya tabbatar da cewa jam’iyyar PDP bata da amfani a jihar a yanzu kuma bazai yiwu jam’iyyar tayi nasara ba.
KU KARANTA KUMA: An zargi Buhari da daukar nauyin harin makiyaya
Cikin yan makonni da suka wuce, Alhaji Abubakar Momoh ya jagoranci dubban mambobin jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) zuwa jam’iyyar PDP.
Momoh wadda ya kasance dan takarar Sanata na jam’iyyar SDP a zaben arewacin jihar Edo ya jagoranci mambobi da magoya bayansa don su bar jam’iyyar domin komawa jam’iyyar PDP a wani yakin neman zabe da akayi a Royal Block dake Auchi, a karamar hukumar Estako West na jihar.
Asali: Legit.ng