Ko Cesc Fabregas zai koma AC Milan ne?
– Chelsea tayi wa Kungiyar AC Milan tayin aron dan wasan tsakiyar nan Cesc Fabregas.
– Gidan talabijin Milan TV ta tabbatar da cewa Dan wasan na so ya cigaba da zama a Kungiyar Chelsea.
Kungiyar Chelsea ta Ingila tayi wa Kungiyar AC Milan tayin aron dan wasan tsakiyar nan na Kasar Sapin Cesc Fabregas, sai dai dan wasan yace fau-fau, ba ya barin Chelsea!
Chelsea ta yi kokarin bada aron dan wasa Cesc Fabregas zuwa Kungiyar AC Milan ta Italiya, sai dai dan wasan na Kasar Spain ba sa da niyyar barin Ingila. Dan wasa Cesc Fabregas ya buga mintuna 12 ne rak a fadin wasannin wannan shekarar, tun zuwan Sabon Kocin Kungiyar Antonio Conte ya fi amfani da N’Golo Kante, Nemanja Matic da dan wasa Oscar a tsakiya.
KU KARANTA: Chelsea na neman dan wasan Inter
Sabon Kocin Kungiyar ya maida dan wasa Cesc Fabregas zuwa benci. Jaridar SportItalia ta rahoto cewa Chelsea tayi wa AC Milan tallar dan wasan na ta Cesc Fabregas mai shekaru 29 a duniya, sai dai kuma Jaridar Sky Sports tace sam, ba haka abin ya faru ba! Skysports ta rahoto cewa Kungiyar ta AC Milan ce ke zawarcin dan wasan Chelsea din Fabregas Cesc.
A tsarin shine dama dan wasa Fabregas zai koma AC Milan aro na tsawon shekara guda, sai Kungiyar ta cigaba da biyan albashin na sa. A lokacin da aka rubuta wannan rahoto, Shugaban Kungiyar ta AC Milan Adriano Galliani, yana tattaunawa da Kocin na AC Milan Vincenzo Montella, ganin yiwuwar wannan ciniki.
Gidan Talabijin Milan TV dai ta tabbatar da cewa dan wasan ba ya da niyyar barin Chelsea ko kadan, asali ma dai yana ganin cewa da yiwuwar Kocin Kungiyar Antonio Conte ya dama da shi a nan gaba.
Asali: Legit.ng