An dauki aron Omeruo daga Chelsea
– Dan wasan Najeriyan nan Kenneth Omeruo, ya koma Kungiyar Alanyaspor daga Chelsea.
– Omeruo yace wannan ba karamar dama ba ce ya samu.
– Wanne ne karo na hudu dan wasan zai bar Kungiyar Chelsea.
Ba a dade ba da dan wasa Kenneth Omeruo ya kara tsawaita kwantiragin sa da Kungiyar Chelsea, sai ga shi Kungiyar Alanyaspor ta Kasar Turkiyya ta dauki aron dan wasan. Dan wasan bayan dai zai tafi aro karo na hudu kenan daga Kungiyar. Kungiyar Besitkas tayi yunkurin karbar aron dan wasan, sai dai makudan albashin sa, suka sa Kungiyar ta hakura. Daga baya kuma Kungiyar Alanyaspor ta dauki aron dan wasan mai shekaru 22 da haihuwa.
KU KARANTA: An Dauki Aron Wasu 'yan Chelsea
Dan wasa Omeruo ya fadawa BBC Sports cewa ya samu damar fito da kan sa ne yanzu. Yace yanzu zai kara kaimi ya kara kuma dagewa da koakri. Omeruo yace: “Ba ni so in rika ji cewa ni dan wasan Chelsea ne… abin da na ke so shine in taimaki Kungiyar Alanyaspor a wasannin ta.” Omeruo ya kara da cewa, ba ya son yayi ‘riga malam masallaci’, yace komai daki-daki yak e faruwa. Yanzu abinda yake so, ya maida hankali, yayi kwallo, kamar kowa.
Dan wasa Keneth Omeruo ya zo Chelsea ne tun shekarar 2012, sai dai har yau bai buga wasa ko day aba, sau hudu kenan ana daukan sa aro. Ko a shekarar bara, dan wasan bayan ya buga kwallo a Kasar Turkiyyar, inda ya bugawa Kungiyar Kasimpasa.
Dan wasa Omeruo ya zo Kungiyar Chelsea ne daga Kasar Beljika inda yake bugawa Kungiyar Standard Liege. Kawo yanzu kuwa, ya bugawa Kungiyoyi da dama, irin su; ADO Den Haag da ke Kasar Netherlands da kuma Kungiyar Middlesbrough ta Ingila aro.
Asali: Legit.ng