Farashin simintin yayi tashin goron zabi
Tamkar sauran kayayyakin masarufi, haka shima farashin siminti yayi tashin goro zabi, farashin ya tashi da kashi 44 inda ya kai naira N2300. Radadin tashin farashin ya zagaya ko ina cikin kasuwa inji jaridar Guardian.
Kamfanunuwan dake hada siminti sun yi karin N600 sakamakon tsadar rayuwa daya sanya farashin abubuwa da suke harka da shi tashi, sai kudin daukan kaya N100. Hakan yasa farashin sari ya tashi daga N1600 zuwa N2300.
Mambobin kungiyar kamfanunuwan masu siminti sun hada da Dangote, Lafarge, WAPCO, Arewa cement, Ashaka da United cement. Tashin farashin siminti na zamowa barazana ga masu karafi wajen kokarin mallakan gidajensu na kansu.
“hakan zai samar da mawuyacin yanayi a bangaren gine gine, wanda zai kawi rashin aminci tsakanin yan kwangila da masu gida, saboda dole ne yan kwangila su kara kudin aiki. “sa’annan hakan zai janyo jinkirin kammala sababbin ayyuka har sai an sake sabon yarjejeniya. A wani hannun kuma, lamarin zai sanya yan kwangila suyi gaggawar kammala aiki saboda tunanin farashin kayayyaki ka iya tashi a kasuwa.” Inji mataimakin shugaban kungiyar magina na kasa Kunle Awobodu.
Kamar yadda wani jami’i a daya daga cikin kamfunuwan hada siminti yace,tashin farashin baya rasa nasaba da matsalar tattalin arziki dake damun kasar nan, don haka kamfanunuwan dake hada siminti zasu yi fama da matsaloli kamar haka:
1. Karancin aiki a kamfani saboda wahalar samun man disil
Tsadar man disil wanda litansa ya kai N130
kokarin daidaita tashin farashin kayan aiki da riba
Wasu daga cikin abubuwan da suka sanya tashin siminti sune:
1. Wahalar samun canjin dala
Asarar dake tattare da canjin dala
Tsadar hada siminti
Karancin wutan lantarki da kuma tsadar sa
Daurewar matsalar samun man disil.
Sai dai a yan kwanakin nan wasu masu ruwa da tsaki a harkar mai da iskar gas suka bayyana cewa a yanzu haka bangaren mai ba wuri bane da ya dace yan kasuwa su zuba jari a wurin saboda matsalolin dake addabar sashin.
A wani labarin kuma, wani shahararren dan kasuwa Mista Atedo Peterside yayi hasashen cewa Najeriya zata dade a cikin wannan halin da tattalin arzikin kasar ke ciki. Peterside ya bayyana cewa masu zuba jari basu son zuba jari a Najeriya sakamakon lalacewar tattalin arzikin kasa.
Asali: Legit.ng