Wasu ‘yan wasan Chelsea za su bar Kungiyar

Wasu ‘yan wasan Chelsea za su bar Kungiyar

– ‘Yan wasan gaban Chelsea biyu za su bar Kungiyar aro.

– Dan wasan na Kasar Faransa, Loic Remy zai koma Kungiyar Crystal Palace.

– Kennedy kuma zai koma Kungiyar Watford ta Ingila.

Wasu ‘yan wasan Chelsea za su bar Kungiyar

‘Yan wasan gaban Chelsea biyu, Loic Remy da kuma dan wasa Kennedy za su bar Kungiyar aro zuwa Kungiyoyin Palace da Watford. Yan wasan na da damar a saye su idan har sun taka rawar gani.

Dan wasan gaban nan watau Loic Remy ya bar Kungiyar Chelsea zuwa Crystal Palace na aron shekara guda, dan wasan mai shekaru 29 ya gaza samun wuri tun da ya koma Kungiyar a kakar wasannin shekarar 2013/14 daga Kungiyar Newcastle bayan ya ci kwallaye har 14.

A wannan shekarar dan wasan ya samu kan sa bayan ‘yan wasa Diego Costa da kuma sabon dan wasa Michy Batshuayi. Remy ya zabi ya koma Kungiyar Crystal Palace tare da Christian Benteke domin kokarin dago Kulob din. Kungiyar Palace dai ta sayi sababbin ‘yan wasa kusan biyar kenan a kakar bana.

KU KARANTA: CHELSEA ZA TA SAYI MARCELO BROZOVIC

Haka kuma dai dan wasan gefen nan na Chelsea Kennedy, ya tattara ya bar Kungiyar. Dan wasan zai koma bugawa Kungiyar Watford a matsayin aro wannan shekarar, dan wasan na damar a saye sa idan har ya taka rawar gani a Kungiyar. Jose Mourinho ne dai ya saye dan wasan daga Kungiyar Fluminese kan kudi fam miliyan £7 a bara, sai dai dan wasan bai burge sabon Kocin Kungiyar ba, Antonio Conte.

Dan wasan dan asalin Kasar Brazil na iya buga gurbin baya da kuma sama (lambar hagu) zai zama sabon dan wasa na 12 da Kungiyar ta Watford ta kawo wannan shekarar. Ana kuma rade-radin cewa Chelsea na ganin yiwuwar sayen dan wasa James Rodriguez na Real Madrid.

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng