Fulani makiyaya ba yan baranda bane – Sarkin Ilori

Fulani makiyaya ba yan baranda bane – Sarkin Ilori

–Sarkin Ilori, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari,ya wanke Fulani makiyaya daga laifuffukan da aka ce suna yi a fadin kasa

–Sarkin yace makiyaya masu zamnalafiya ne, kuma da kyakkyawan alaka na zamantakewa da bare.

–Yana kira ga jama’a da su yi bincike akan abu kafin fara yada abin da zai kawo rashin jituwa a kasa.

Fulani makiyaya ba yan baranda bane – Sarkin Ilori

Sarkin Ilori, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari,ya tsarkake  Fulani maiyaya daga laifuffukan da ake jingina musu na kai hare-hare a fadin kasa. Sarkin yace makiyaya masu zaman lafiya ne, kuma da kyakkyawan alaka na zamantakewa da bare. Yana kira ga yan najeriya da su cigaba da zaman lafiya domin samun hadin kai.

Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari yace hare-haren ake kaiwa a fadin kasa da sunan Fulani makiyaya . Yace babu gaskiya a cikin maganar cewa Fulani makiyaya na da alhakin hasaran rayukan mutane da dukiyoyi a wasu sassan najeriya kana Fulani na da kyawun zamantakewa.

Sarkin gargajiyan ya fadi hakan jiya yayinda mambobin unguwar Balogun Gambari suka kawo masa ziyaran ban girma saboda Karin matsayin Balogun Gambari a Ilori, Alhaji Adedayo Balogun,a matsayin babban jigo a masarautan ilori.

KU KARANTA : Dubun wani dan tasi ta cika yayin da yake so ya sace wani fasinjan sa

A bangare guda,gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ,ya sanya hannu a cikin sabuwar doka na haramta wa Fulani makiyaya a yankin kudu maso yamma. Ya sanya hannu ne a ranan litinin, 29 ga watan agusta a gaban sarakunan gargajiya kimanin 3.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: