Wani fasto yayi luwadi da dan shekara 13
An kai karan wani fast wanda yayi fyade wa wani yaro dan shekara 13
Game da rahotanni, faston cocin Jesus Miracle Ministries da ke Awka,jihar Anambra,ya arce yayinda aka fara zarginshi da yin luwadi karfi da yaji da wani yaro dan shekara 13. Game da wata majiya wanda aka sakaye sunan, faston ya je wajen wani boka ne wanda ya fada masa cewa yayi luwadi da yaron domin magance cutan luwadinsa.
Ga abinda yaron yace mai suna Abuchi :
“Faston ya zo wurina bayan wani adduan dare yace mini in tsaya. Na fada ma faston cewa ina son in koma gida tunda an gama addua. Faston ya fada mini in tsaya har wayewan gari. Da nan ace cewan sai na tafi,sai ya fesa mini wani abu wanda ya sani bacci . da na tashi sai nag a cewan wando nay a yage,kuma dubura nay a jike. Sai na fara kukasaboda ina jin zafi a dubura na. faston yace in daina kuka,cewa zai bani kudi. Sai na ki kudin na tafi gida na fada ma iyayena abinda ya faru.”
Daya daga cikin yan uwan Abuchi, Ngozi ta bayyana cewa basu san yaron ya je coci a daren nan,ar lokacin da ya fada musu abinda ya faru. Kuma da suka koma cocin ,basu ga faston ba.
Kakakin yan sandan jihar Anambra ,Nkiru Nwode tace yan sanda na bin dan sandan kuma za’a kama.
Asali: Legit.ng