Muhimman labarai daga jaridun Najeriya
Muhimman labarai da sukayi fice daga jaridun Najeriya a yau Litinin 29 ga watan Augusta, domin jin dadin masu karatu.
Binciken da jaridar Daily Trust tayi ya bayyana cewa kasar Najeriya ta yi asarar sama da naira triliyan 1.1 a kudin man petir cikin watanni biyar da suka wuce sakamakon harin yan bindiga suka kai a bututunan mai.
An samu akkala hare-hare 25 a bututunan mai daga ranar 10 watan Fabrairu na shekara 2016 zuwa karshen watan da ya gabata daga tsagerun niger delta avengers.
Jaridar New Telegraph ta ruwaito cewa shugaban kasa muhammadu Buhari ya kuma, shan alwashin maganin yan bindigan Niger Delta kamar yadda gwamnatinsa ta magance yan kungiyar Boko Haram idan suka ki ba da hadin kan tattaunawa da gwamnatin tarraya.
Buhari yace hankalin gwamnatinsa a yanzu ta karkata ga dakatar da lalata tattalin arzikin kasa da yan bindiga keyi a yankunan dake da albarkatun man petir.
Daga karshe Jaridar Daily Sun ta ruwaito cewa gurare da dama sun samu ambaliyar ruwa a jihar Lagas sakamakon ruwan sama da akayi a fadin jihar a karshen mako.
Gurare kamar su Gbagada, Lekki, Oworonshoki, Shogunle, Ikorodu, da kuma Ifako sun samu ambaliyar ruwa sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya, wanda aka fara a daren ranar Asabar har ranar Lahadi. Ya kuma yi asarar dukiya na miliyoyin naira.
Asali: Legit.ng