Kalla yadda Yar Edo Ta Sace Ma Dan Italy zuciya.
-Irene Adam sun hadu, sai suka fara soyayya.
-Irene ta kawo Luca gida Edo , Dan ai masu auren Edo na gargajiya.
-Luca ya tafi da Irene kasar Italy dan auren su na fararen kaya a bakin ruwa.
Irene tayi aure da mijin ta abin kaunarta dan kasar Italy makon da ya gaba ta wanda ake kira da suna Luca Tomosi. Sun yi auren Edo na gargajiya a kasar Najeriya. Su ka kammala auren na farin kaya a kasar Italy a bakin ruwa.

Bikin da akayi, Luca ya zo da mutanen shi tun daga kasar turai zuwa Najeriya dan taya shi murna , bayan bikin kuma ya dauki matar zuwa kasar turai dan fara sabuwar rayuwa.

Shi kuma bikin farin kayan da aka yi Irene ta saka kayatattun kaya masu kyau farare ,haka ma Luca. Ma'auratan sun bayyana a hoto suna cikin farin ciki ,da fuskokin su dauke da murmushi . Wannan ya nuna ma'auratan suna cike da kaunar juna, kuma sun farin cikin fara sabuwar rayuwa a matsayin mata da miji.

Asali: Legit.ng